News

Ƴan Sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan fashin dajin Jahar Zamfara, Mai-ƴanmata a Zamfara

Ƴan Sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan fashin daji, Mai-ƴanmata a Zamfara

Rundunar Ƴan Sanda ta Jihar Zamfara ta tabbatar da cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji, Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-ƴanmata a jihar.

Rundunar ta ce Mai-ƴanmata, ɗan shekara 20 kacal da haihuwa, ya ƙware wajen garkuwa da mutane, fashin daji, satar shanu da sauran manyan laifuka a yankin Shinkafi, Zurmi da Birnin Magaji a Zamfara.

Kwamishinan Ƴan Sanda na Jihar Zamfara, Ayuba N. Elkanah ne ya baiyana haka a taron manema labarai yayin da rundunar ta yi holon ɗan ta’addan a juya Laraba.

A cewar Kwamishinan, ” a ranar 28 ga Disamba da misalin ƙarfe 5 na yamma, yayin da su ke wani sintiri na sirri bayan sun samu bayanan sirri, sun cafke wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Sani Mati, wanda a ka fi sani da Mai-ƴanmata ɗan ƙauyen Mayasa a Ƙaramar Hukumar Zurmi.

Ya ƙara da cewa Mai-ƴanmata ya shiga komar ƴan sanadan ne lokacin yana shirin sanya shinge ya tsare bayin Allah domin ya yi garkuwa da su a daidai wani ƙauye mai suna Koliya.

Elkanah ya ƙara da cewa da a ɓangaren Turji Mai-ƴanmata ya ke, inda yanzu ya koma sansanin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Kachalla Sani Black.

Ya ce an samu bindiga samfurin AK-47, sai kwanson harsashi 2, sai harsashi 3 da kuma babur guda 1.

Ya ce a na nan a na yi masa tambayoyi inda da ga nan za a ki shi kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button