YANZU-YANZU: Musulunci ya samu ƙaruwa da manyan Fastoci 42 da iyalansu a Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa addinin musulunci ya samu ƙaruwa da Fastoci 42 tare da matayensu da wasu Bishop biyu da matayensu suma.
Sai wata Fasto ɗaya mace da sista, inda suka karbi musulunci a babban ɗakin taron babban masallacin ƙasa dake babban birnin tarayya Abuja.
Jaridar Daily Trust Hausa Ta Wallafa A Shafinta Na Facebook Cewa.
Bisa bayanai da majiyar mu ta Zuma Times ta samu, an shirya musu taro na musamman domin ilmantar da su.
Har na kwanaki bakwai a dakin taro na babban masallacin dake Abuja.
Al’ummar musulmai ne daga fadin duniya suka tayasu murna tare da yimusu addu’ar Allah yasa an shigo a sa’a
Inda wadansu suka shawarcesu Da Sai sunyi hakuri domin zasu fara ne da cin karo da jarabawar ubangiji.