YANZU-YANZU: Hukumar EFCC ta sake binciko wasu sabbin N90 biliyan bayan N80 biliyan da ake zargin AGF Ahmed Idris da handama, jimilla ta kai N170 biliyan a yanzu.
A yayin bincikarsa, Ahmed Idris ya bayyana sunan wani minista tare da wasu manyan jami’an gwamnati da ke da hannu wurin damfarar N170 biliyan.
An gano cewa, Idris yana bada hadin kai wurin binciken inda a halin yanzu har an gayyaci wani sakataren gwamnatin tarayya da Idris ya ambata.
Majiya ta sanar da cewa, Idris ya sha alwashin mayar da wasu tsabar kudi zuwa lalitar gwamnati yayin da ya ke rokon EFCC da ta bada belinsa.
Kamar yadda binciken jaridar The Nation ya bayyana, jami’an EFCC sun bankado wasu manyan almundahanar kudade daga ofishin akanta janar din.
An tattaro cewa, duk da a farko ana zargin AGF din da wawurar kudade har N80 biliyan, bincike ya nuna cewa akwai karin wasu N90 biliyan.
Me za ku ce?