News

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar-ta-ɓaci a ƙananan hukumomi 2

YANZU-YANZU: Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar-ta-ɓaci a ƙananan hukumomi 2

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar-ta-ɓaci ta tsawon sa’o’i 24 a Ƙananan Hukumomin Jema’a da Kaura, inda ta ce tuni dokar ta fara aiki.

Sanarwar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan.

Sanarwar ta ce an dauki wannan mataki ne biyo bayan shawarwarin da hukumomin tsaro suka bayar da kuma taimakawa jami’an tsaro don daidaita al’amura da kuma dawo da doka da oda a yankunan.

Ta kuma bayyana cewa, hukumomin tsaro na da cikakken ikon aiwatar da dokar-ta-ɓacin, inda gwamnati ta yi kira ga ɗaukacin mazauna Ƙananan Hukumomin Jema’a da Kaura da su baiwa jami’an tsaro hadin kai don dawo da zaman lafiya da bin doka da oda cikin gaggawa.

Hakazalika sanarwar ta ce gwamnati ta yi Allah-wadai da tashe-tashen hankula da kuma duk wasu ayyukan ta’addanci da suka afku a yankin, domin za a fitar da karin bayani nan gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button