Rahotanni da muke samu yanzu yanzu daga shafin jaridar Aminiya.
Na cewa yanzu haka ana can ana gwabza kazamin fada da sojojin nigeria dakuma yan boko haram a Damasak dake jahar borno.
A yayinda Al’ummar musulmi ke tsaka da azumin watan ramadan
Kungiyar boko haram da ta dade tana salwantar da rayukan dubban nin yan nigeria
Na chan na gwambza fada da dakarun sojojin nigeria a yankin Damasak kamar yadda jaridar Aminiya ta wallafa a shafinta na Facebook.
Sai dai har izuwa yanzu babu wani cikakken rahoto game da asarar rayuka ko kuma raunuka.
Idan kuna bibiyar mu insha Allahu zakuji mu dauke da karin bayani game da lamarin.