YANZU-YANZU: An Saki Sheik Abdulaziz Dutsen Tashi Bayan Tsawon Kwanaki Yana Tsare A Gidan Yari A Jihar Bauchi
Cikin Wata Sanarwa Da Fitaccen Dan Gwagwarmayar Nan Wato Datti Assalafy Ya Wallafa A Shafin Sa Na Sada Zumunta.
Inda Ya Rubuta Cewa, DAGA ALLAH NE
Ina mai farin cikin sanar da ‘yan uwa Ahlussunnah cewa Kotu ta bada belin Malam Idris Abdul-Aziz Bauchi yanzun nan, an saki Malam, ina kyautata tsammanin Malam zai jagoranci Sallar juma’a yau Insha Allah
Da ma na fada muku cewa ku jira zuwa yau juma’a ku ga abinda zai faru da Malam yayin da dakarun Sunnah na Afirka karkashin jagorancin Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau suka motsa
Kai dai ka dogara ga Allah, Ka yi don Allah, Ka nemi agaji da taimakon Allah a inda Allah kadai ke da hakkin taimakawa, Allah Zai isar maka
AlhamdulilLah