‘Yadda Aka Kashe Mijina Musulmi Mahaddacin AlKur’ani Kan Zargin Wi Wa Annabi batanci’
Batun batanci ga addini a sassa daban-daban na duniya wani batu ne mai sarkakiya da ke bukatar taka-tsantsan.
Addinai da kasashe na da dokokin hukunta batanci ga addini.
A kasashen da ke bin tsarin shari’ar Musulunci an tanadar da hukuncin kisa.
A jihohi da dama na arewacin Najeriya ma – inda ake amfani da tsarin na shari’ar musulunci da kuma dokokin kasa a lokaci guda – an tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi batanci ga addinin Islama.
To amma wani batu da a baya-bayan nan ke sake janyo cece-ku-ce da tayar da jijioyin wuya shi ne yadda wasu fusatattun mutane kan far wa wadanda aka zarga da yin batanci ga addinin Islama.
Akalla mutane biyu ne aka kashe a yanayi mai sarkakiya a baya-bayan nan.
An kashe wata daliba kirista a Sakkwato mai suna Deborah Emmanuel, da kuma wani matashi musulmi mai suna Ahmad Usman a Abuja babban birnin kasar.
BBC ta zanta da iyalan wadanda lamarin ya shafa kan halin da suka shiga – da kuma malaman addinai kan wannan batu.
“Kun cuce ni, kun cuci rayuwata”
Ba mabiya addinin Kirista ne kaɗai fusatattu kan far wa ba dangane da batun ɓatanci ga addini.
Cikin watan Yuni, wasu wadanda suka harzuƙa sun far wa wani matashi Musulmi mai suna Ahmad Usman, suka lakaɗa masa duka, suka kashe shi, kana suka ƙona gawarsa bisa zargin cewa ya yi ɓatanci ga addinin Musulunci.
Lamarin ya faru ne a unguwar Lugbe da ke Abuja babban birnin Najeriya.
Na ziyarci gidansu Ahmad, inda na tarar da ƴan uwa da abokan arziki na cikin jimani – cikinsu har da matarsa Zainab, mai zaman takaba.
Watansu takwas da aure kafin a kashe shi. Tana da juna biyu, tana fatan samun ɗansu na fari kuma na ƙarshe.
Zainab na zub da hawaye, dangi na rarrashinta. Ta musanta zargin da aka yi wa mijin nata, tana mai cewa ƙazafi ne.
Ahmad mai shekaru 30 da haihuwa, ɗan banga ne.
Bayanai sun nuna cewa yayin da Ahmad ke sintiri, sai suka yi jayayya da wani malamin addinin Musulunci kan bukatar malamin ya kiyaye dokar hana fita da dare.
Daga nan Malamin ya zarge shi da yi wa addinin Musulunci ɓatanci.
Washegari kuma fustattun suka kashe Ahmad a kusa da ofishin ƴan bangar.
Abokan aikinsa sun ce mutum ne mai himma
Abokan aikinsa sun ce zaƙaƙurin jami’i ne.
“Wannan ƙazafi da suka yi masa, shi ne ya fi damuna a zuciya’’ a cewar Zainab.
“A kullum mijina ba shi da wata magana sai dai ka ji ya ce ‘mu yi wa Annabi salati’ kuma shi mutum ne da ya haddace Alkur’ani a kansa.”
Ta haƙiƙance cewa babu yadda mai gidan nata zai yi wa Annabi ɓatanci.
Mai dakin Ahmad ta ce saboda irin yadda take jin zafin wannan “ƙazafi” ba za ta yafe wa wadanda suka kashe mata miji ba – amma ta roki Allah “Ya shiryi masu irin wannan hali’’ na ɗaukar doka a hannu ba tare da hujja ba.
“Sun cuce ni, kuma sun cuci iyayensa’’ in ji matar mai juna biyu. Ta yi imanin jajircewarsa a kan aiki ne ya aka yi masa “sharri” kuma lamarin ya kai ga kashe shi.
Zainab ta ce a marainiya ta taso, iyayenta sun rasu tun tana jaririya.
Tana daukar mijin nata tamkar “uwa da uba” saboda yadda yake kula da ita yana kuma tausaya mata, yana share mata hawaye.
Ta ce wadanda suka kashe shi “sun cuce ni, sun cuci iyayensa” kuma yanzu “ban san yadda rayuwa zata kasance mini ba.’’
Wasu labaran da za ku so ku karanta
Malama Zainab Ahmad ta kuma nuna bacin rai kan yadda fusatattun suka ƙona gawar mijinta bayan sun kashe shi tana mai cewa “Allah ne kadai ke hukunci da wuta, ba mu ba.’”
Ta bayyana lamarin a matsayin tsabagen nuna tsana tana mai cewa “ƙiyayyar ta yi yawa.”
A ganinta, sun yi masa ƙazafi ne saboda ƙoƙarinsa na tabbatar da bin doka a aikinsa na ɗan sintiri.
Zainab ta ce a kullum ‚‘ko na rufe idona sai in riƙa ganinsa, kamar yana nan.‘
Yanzu hotunan mijinta ke ɗebe mata kewa, musamman hotunan da yake murmushi kuma kullum tana yi masa addu’ar samun rahama.
Ta kara da cewa babban fatanta yanzu shi ne Allah Ya taimake ta ta haihu lami lafiya kasancewar mijinta ya bar ta da juna biyu, kuma shi ma kafin mutuwarsa “burinsa shi ne ya ga abin da zan haifa.”
Shi kuwa Usman Shehu wanda shi ne mahaifin Ahmad, ya shaida wa BBC cewa ya ma kira ɗan nasa a waya a lokacin da ake kashe shi.
An amsa kiran, amma Ahmad din bai samu damar yi masa magana ba.
Mahaifin ya ce bai san me ke faruwa ba a lokacin, illa ya ji kwarmniya da ƙarar duka da sara.‘kat! kat!! kat!!
Sai daga bisani aka shaida masa cewa an kashe ɗan nasa. Lamarin ya dugunzuma shi da ma sauran dangi.
Malam Shehu ya bayyana Ahmad a matsayin gatansa saboda yadda yake kula da shi.
Ya bayyana Ahmad a matsayin ‘ɗa mai ƙwazo, ya ƙara da cewa “gaskiya na yi babban rashi. Har in koma ga Allah ba zan manta ba.”
Hukumomi dai sun bayyana cewa suna gudanar da bincinke dangane da kashe Ahmad Usman kuma an kama wasu da ake zargi yayin da iyalansa ke fatan a yi adalci a lamarin.