Yadda ƴan bindiga suka kashe hakimi suka tayar da gari a Zamfara Tare Da Kashe Mutane Da Dama
Ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutum 25 da suka haɗa da Hakimi da wasu sarakunan gargajiya a ƙaramar hukumar Bukkuyyum a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Ƴan bindigar sun abka ƙauyen Ganar Kiyawa ne a ranar Lahadi suka kashe mutanen, kamar yadda mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Mutanen garin sun ce ƴan bindigar sun shiga garin na Ganar Kiyawa ne saman babura, kuma bayan mutane sun tsorata sun fara tserewa, ƴan bindiga suka dinga harbinsu, cikin waɗanda aka kashe har da hakimin garin Bala Muhammadu da Magajin gari Sani Salihu da wani bafade da ake kira Sharu.
“Da ni da Hakimi da Magajin Gari mun yi gudun kilomita uku, kuma da suka cimma Magajin Gari suka tambaye shi me yake wa gudu ya ce wahala, sai suka ce to ta ƙare, suka harbe shi,” a cewar wani mazauni garin da yake bayar da labarin da ƴar magajin garin da aka kashe ta faɗa masu bayan sun tsira.
Maharan sun tarwatsa garin Ganar Kiyawa inda dubban mutane suka tsere zuwa wasu ƙauyuka makwabta.
Hakimin Adabka ya shaidawa BBC cewa mutanen da ke cikin garinsa sun kai kusan mutum 3,000.
A cikin wata sanarwa bayan kai harin, gwamnatin jihar Zamfara ta jajantawa mutanen garin tare da bayar da umarnin kai masu tallafi.
“Mun biya ƴan bindiga miliyan uku”
Mazauna garin Ganar Kiyawa sun daɗe suna fuskantar hare-haren ƴan bindiga a kwanakin baya bayan nan.
Sun ce sun biya kuɗi kusan miliyan uku da ƴan bindigar suka tilasta masu.
Wani mazauni garin wanda ya ce an kashe masa ƴaƴa bakwai ya ce: “mun biya naira kusan miliyan uku na fansa da suka ce dole sai mun biya.”
Da farko ya ce maharan sun fara kore shanu ne daga baya suka dawo suka sake shiga gidaje suka ce sace mutane suka ce dole sai an biya kudi miliyan uku da wasu dubu dari.
Mutanen garin sun ce duk da sun biya kuɗin amma ba su iya barci cikin kwanciyar hankali.
Tun watan Janairu Jami’an tsaro ke kai farmaki a yankin domin kakkabe ƴan bindigar.
Ƴan bindiga da ke ɓuya a dajin Gando sun daɗe suna kai hari a ƙauyukan ƙananan hukumomin Bukkuyyum da Anka.
Jihohin arewa maso yammaci na Zamfara da Kebbi da Sokoto sun daɗe suna fuskantar hare-hare na ƴan bindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa.