Direban tasi zai shafe watanni 30 a gidan yari sakamakon kaɗe ƴar sanda da mota
Wata Kotun Majistare a yau -Juma’a ta yanke wa wani Adelaja Ogundairo, direban tasi, hukuncin daurin watanni 30 a gidan yari da kuma yi wa al’umma hidima na tsawon watanni uku bisa samunsa da laifin tukin ganganci tare da buge wata ƴar sanda.
Mai laifin, a lokacin da ake shari’ar, ya ki amsa laifuffuka ukun da ake tuhumarsa da su ka haɗa da tukin ganganci, kin bin dokokin hanya, da kuma jikkata wata ƴar sanda da ke bakin aiki yayin da ya ke tuki ba tare da lasisi ba.
Alkaliyar kotun, I. O. Abudu, ta samu Ogundairo da laifi kuma ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni 12 da kuma yin hidima ta tsawon watanni uku a harabar kotun, saboda laifin tukin mota mai hatsari.
Abudu ta kuma yanke hukuncin daurin wata 12 a gidan kaso na biyu bisa tuhume-tuhume na biyu da ya hada da yi wa ƴar sanda rauni da kuma rashin kai rahoton hadarin.
A tuhuma ta uku, Alkaliyar kotun ta yanke masa hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa samun sa da laifin tuki a kan babbar hanyar jama’a ba tare da lasisin tuki ba.
Abudu, ta ba da umarnin cewa hukuncin zaman gidan yari na watanni 30 da yi wa al’umma hidima na wata uku a lokaci guda ba tare da wani zabi na tara ba.
Ta kuma umurci wanda aka yankewa hukuncin da ya biya diyyar N50,000 ga ƴar sandan da ya kade har ta samu rauni, inda ta ce kudaden na magani ne da ta yi a lokacin jinya.
Tun da fari dai, mai gabatar da kara, Sifeto Lawrence Olu-Balogun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 21 ga watan Nuwamba, 2021 da misalin karfe 11:00 na safe a hanyar Lafenwa a Abeokuta.
Olu-Balogun ya ce wanda aka yanke wa hukuncin ya saba wa ka’idojin zirga-zirga, ta hanyar tsayawa a tsakiyar titi da daukar fasinjoji.