Wasu ‘Yan Jigajigan Jam’iyyar NNPP Sun Fasa Kwai, Za Su Binciki Su Kwankwaso a Kan Bacewar N1bn
Anjuyo Kan Kwankwaso Za’a Binciki Inda Naira Biliyan Daya Suka Shige – NNPP
NNPP za ta yi bincike a kan yadda aka yi fatali da fiye da Naira biliyan daya da aka samu a fam.
An yanke shawarar a gayyato hukumomin tsaro su yi binciken asusun jam’iyyar NNPP da kyau.
Hakan zai iya jefa ’dan takarar shugaban kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da mutanensa a matsala.
Wasu ‘Yan NNPP Sun Fasa Kwai, Za Su Binciki Su Kwankwaso a Kan Bacewar N1bn
Sakataren yada labaran ‘yan taware a jam’iyyar, Abdulsalam Abdulrasaq, ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar bayan sun yi zama a sakatariyar kasa.
Jawabin ya ce za a bi diddikin duk wasu kudi da aka zargin an batar tun daga 2022 zuwa yanzu.
“NNPP za ta yi bincike da kyau a kan yadda aka yi fatali da fiye da Naira biliyan daya da aka samu daga saida fam ga masu shirin takara daga Maris na 2022 zuwa yau.
Taron ya yanke shawarar a gayyato hukumomin tsaro su yi binciken asusun jam’iyyar da kyau da nufin samun bayani daga ’dan takarar shugaban kasa da tsohon shugaban jam’iyya wanda ya tafi a watan Maris 2023, shugaban rikon kwarya da aka tsige da kuma sakatare na kasa.
Jawabin kamar yadda Punch ta rahoto, ya ce binciken zai kara karfin gwiwar ‘yan jam’iyya, masu shirin shiga takara su iya fitar da kudi domin sayen fam.
Abdulrasaq ya kuma soki yadda aka kafa dakin bibiyar zaben sakamakon zaben 2023 a gidan wanda ya yi wa jam’iyyar NNPP takarar shugaban kasa a 2023.
An zargi jam’iyyar da rashin adalci wajen tsaida ‘yan takara, saboda haka za a kafa kwamiti da zai binciki Injiniya Buba Galadima wanda jigo ne a NNPP.