News

Wasu Kayatattun Motocin Alfarma Da Ake Sana’ar Taxi Dasu Babban Birnin Yamai Na Jamhuriyar Niger

Wasu Motoci Da Ake Sana’ar Taxi dasu a jamhuriyar Nijar Sun Dauki Hankalin Jama’a Da Dama Tare Dasasu Tofa Albarkacin Bakinsu Game Da Lamarin.

Rahotanni Sun Bayyana Cewa Wannan Dalla Dallan Motocin Ana Gudanar da Sana’ar taxi dasu ne a birnin yamai dake jamhuriyar nijar.

Lamarin da ya jawo cecw kuce tare da sa matasa tofa Albarkacin bakin su akai.

Dafari dai Shafin Damagaran Post ne suka wallafa cewa. Taxi a birnin Niamey, birnin da yafi kowane tsadar rayuwa a Niger da ma yankin UEMOA.

To Sai Dai Mutane da dama Musamman ma wadanda basu taba ziyartar kasar ta nijar ba sun karyata lamarin tare da yin bakaken maganganu,

Yayin da A Gefe Guda Kuma Wasu mazauna Babban Birnin Na Yamai Suka Shiga Sa’insa Da Mutanen Dake karyata batun tare da yiwa kasar su ta nijar kallon Marasa Arziki.

Kasar Nijar dai kasace da tasha Fama Da Matsin Tattalin Arziki A Shekaru da dama da suka gabata.

To sai dai a yanzu za’a iya cewa kasar tafita daga matsin Tattalin arzikin da ta tsinci kai a shekarun baya.

Wani rahoton da Bankin Duniya ya fitar ya ce Jamhuriya Nijar ta fita daga jerin kasashe matalauta a nahiyar Afrika, inda ma yake cewa duba da yadda al’amura ke gudana a kan abin da ya shafi tattalin arzikin kasar, akwai yiwuwar kasar za ta samu ci gaba da ya zarta haka ta fannin tattalin arziki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button