Tun bayan faruwar rikicin fadan kabilanci da ya faru a jahar oyo. Wanda ya kai ga mutane da dama sun rasa rayukan su tare da asarar dukiya mai dimbin yawa wanda galibin dukiyoyin na yan Arewa ne mazauna Garin na Oyo.
Mutane da dama sun fito sunyi Allah wadai da wannan rikicin a shafukan su na sada zumunta. Ciki kuwa harda wasu daga cikin manyan jaruman kannywood.
Hausawa 10 ne suka rasa rayukan su a yayin rikicin yayinda Mutum sama da dari suka jikkata.
Andai ta kiraye kiraye tare da fadin cewa yankin Arewa ya rasa masa daga murya aji akan wannan rikici dama cin mutumci daa mutanen kudu ke yiwa yan Arewa.
Hakan tasa jarumi Adam a zango yai wata wallafa a shafin sa inda yake cewa.
Wa kuke so yayi magana kuma yanzu?
1. Prof Ango Abdullahi yayi magana kun zage shi.
2.Malam Ja’afar yayi huduba da irin yaren da Gwamnati tafi saurara akan irin wannan yanayi da ake ciki a 2004 amma aka samu wasu ‘Yan iskan yara (zauna gari banza) suka datse Audio suka yanko inda yafi yamutsa hazo, suka dora wai Dan Ta’adda ne, yana koyar da ta’addanci.
Yanzu kuma kuna maganar an rasa wanda zaiyi magana. Maganar ***** ku za’ayi.