Tunda Na Fassara Al-Qur’ani Zuwa Harshen Igbo Yan Kabilar Suka Tsane Ni
Kamar yadda kuka sani a kwanakin baya akwai wani bawan Allah wanda ya fassara al-qur’ani zuwa harshen Igbo wanda mutane suke ta sa masa albarka.
Sai dai kuma labarin da muke samu shine shi alaraman ya koka inda yace:
“Tunda na fassara Al-Qur’ani Zuwa harshen Igbo, Kabilun Suka Tsane ni inji malam Mustapha“
Sheikh, Alh, Mustapha Wanda ya fassara Al-Qur’ani Mai Tsarki Zuwa harshensa na Igbo, a cewarsa yayi hakanne ta yadda Igbo Zai Karanta ya Kuma gane a domin ya amshi Musulunci ya Kuma San ya Addinin Musulunci yake.
A wata Hira da yayi da manema Labarai, Alh. Mustapha ya bayyana masu cewa, ‘Yan uwansa na kusa sun Yi matukar Farin ciki da irin wannan Babar Nasarar da yayi na fassara Al-Qur’ani Zuwa harshen Igbo, Kama hausawa, Yarbawa duk sun yi Shukur da wannan babbar Nasara.
Bugu da Kari amihad.com taci gaba da bibiya lamarin, inda yaci gaba da bayyana cewa, wasu ne daga cikin Kabilun na igbo Da su ba Musulmai bane Suka addabesa da habaici iri-iri.
Dalilin Dayasa Ya Fassara Al-Qur’ani Zuwa Harshen Igbo
Malam Muhammad Murtala Chuwkuemeka ya zama abin magana bayan ƙaddamar da fassarar Al-qur’ani cikin harshen Igbo da yayi wanda ya fara aikin sa shekara biyar da suka gabata.
Ɗan asalin jihar Imo wanda ya musulunta shekara 33 da suka wuce ya bayyana cewa ya fassara ayoyi 6,236 na Al-Qur’ani mai girma.
Ya bayyana dalilan sa
A wata da hira tashar BBC News Pidgin, Chuwkuemeka ya bayyana cewa yayi hakan ne domin yana son Inyamurai su san addinin musulunci.
Ya bayyana cewa:
Na fassara Al-Qur’ani zuwa harshen Igbo domin ina son Inyamurai su san addinin musulunci don suna kiran shi a matsayin addinin Hausawa, Yarbawa da Larabawa
Ba su yarda cewa musulunci na kowa bane. Akwai Al-Qur’ani na Hausa, Al-Qur’ani na Yarbanci, Al-Qur’ani na Turanci amma babu na yaren Igbo kafin yanzu.
Ya samu yabawa sosai daga Hausawa da Yarbawa
Malamin yace ya samu yabawa sosai daga Hausawa da Yarbawa fiye da Inyamurai
Wasu Hausawa da Yarbawa da suka karanta fassarar Al-Qur’ani na zuwa harshen Igbo sun ji daɗi matuƙa
A gaskiya, sun ji daɗi sosai fiye da ƴan’uwana Inyamurai. Wasu daga cikin su sun ce za suyi amfani da Al-Qur’anin su koyi yaren Igbo.
Ya nuna godiyar sa ga al’ummar musulmai
Yayin da yake bayyana cewa Suratul Baqarah itace Surar da tafi tsawo a littafi mai tsarki da ya fassara, ya fassara ta cikin shekara biyu. Chukwuemeka ya godewa al’ummar musulmai bisa taimakawa wurin samun nasarar da yayi.
Da al’ummar musulmai ba su ƙarbeni a matsayin Inyamuri ba, da ban samu nasarar fassara Al-Qur’ani ba.