A ranar Litinin ɗinnan Shugaban Najeriya Muhammdu Buhari ke ƙaddamar da matatar mai ta Dangote, wadda ke da ƙarfin tace mai ganga dubu 650 a rana.
Kuma za ta samar da abubuwa kamar man fetur (PMS) da man dizil (AGO) da man jirgin sama da kalanzir da ma wasu abubuwan da dama.
Shugaban matatar, Sanjay Gupta ya ce matatar ita ce irinta mafi girma a duniya.
Wasu masana na cewa matatar za ta samar da ayyukan yi ga mutane da dama a Najeriya.
1. Bayani daga rukunin kamfanonin Dangote sun ce matatar ita ce irinta mafi girma a duniya inda za ta rinƙa tace ganga 650,000 ta ɗanyen mai.
2. An gina matatar ne a yankin Ibeju-Lekki na jihar Lagos a filin da ya kai fadin eka 2,635.
3. Matatar tana da manyan tankuna 177 waɗanda za su iya ɗaukar mai da yawansa ya kai lita biliyan 4.742.
4. Idan ta fara aiki ɗari bisa ɗari za ta iya tace duk man fetur da ake buƙata a Najeriya har ma a samu rara da za a fitar zuwa wasu ƙasashe a kullum.
5. An tsara ta yadda za ta iya sarrafa nau’uka daban-daban na ɗanyen mai daga ƙasashen Afirka da na ƙasashen Gabas ta tsakiya da yankin Amurka.
6. Wani bayani da rukunin kamfanonin Dangote ya fitar ya ce an yi amfani da na’urorin yashe ƙasa mafiya girma a duniya, inda aka yashe ƙasa mai yawan gaske a wurin, aka kuma kashe kuɗi kimanin yuro miliyan 300 a aikin.