Rahotanni Daga Jahar Kano Na Aƙalla mutane 10 ne suka shiga hannu lokacin da suka yi ƙoƙarin kai hari wani masallaci a yankin Hotoro.
Kamar yadda jaridar vanguard ta rawaito cewa. Jami’an sojijin sun ɗauke wasu abubuwa da basu yarda da su ba a kewayen Wani masallaci kafin daga bisani su yi Awon gaba da mutanen da ake zargin.
Rahotanni sun cigaba da bayyana cewa sojojin sun kama mutanen ne adai dai lokacin da suka kutsa Filin Lazio dake yankin Hotoro a cikin garin Kano a yammacin ranar Asabar.
Ankama su suna koƙarin kai hari ne a wani masallaci da kuma wasu gidaje dake yankin, sai dai rahotanni sun kara da cewa farmakin yazo A dai-dai lokacin da Al’ummar musulmai ke shan ruwa bayan sun kai azumin ramadan yayin bude baki.
Shidai Masallacin da akai Yunkurin Kai Harin An Gano Cewar mallakin wasu mutane ne yan asalin jahar Borno ne, waɗanda suka baro gidajensu saboda rashin tsaro da zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabas din.
Haka zalika kuma, An gano cewa jami’an sojojin, sun tattara wasu abubuwa da ba’a kai ga gane su ba a kewayen masallacin. Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar sojojin, Mohammed Yerima, yayi alƙwarin yiwa manema labarai bayani ranar Lahadi.