Religion

BIDIYO: Shugaban kungiyar kungiyar Izalah a Najeriya ta ya yi Allah wadai da abinda ya faru a jihar Sokoto

Shugaban kungiyar kungiyar Izalah a Najeriya ta ya yi Allah wadai da abinda ya faru a jihar Sokoto

Bala Lau yace hukuma ce ke da hurumin yanke hukunci ga wanda ya zagi Annabi, ba ‘dai’daikun mutane ba.

Ya kuma yi kira ga Hukumomi da su dinga zartar da hukuncin kisa ga wanda ya zagi Annabi (S) kafin jama’a su kai ga nasu hukuncin, Wannan ne kadai zai hana’dai’daikun mutane daukar mataki na kisa.

A jawabin da kungiyar ta saki, ta ce yarinyar ta kunduma ashariya ga Annabi (SAW) wanda duk musulmi bazaiji dadi ba, wanda hakan har yakai ga wasu jama’a suka kasheta kuma suka kona ta.

“Addinin musulunci bai bada dama ga musulmi ya zagi ko wane Annabi daga Annabawan Allah ba, dan haka akwai bukatar shugabannin kiristoci su dauki aniyar wayar da kan mabiyansu akan illar taba mutunci ko zagin fiyayyen halitta wanda hakan ka iya tayar da husuma a cikin kasa.”

Shugaban Izalah, Sheikh Bala Lau, yayi kira na musamman ga hukuma da ta dinga saurin daukan mataki na kisa ga wanda ya zagi Annabi (S) da wannan shi zai hana jama’a daukar nasu matakin, amma jama’a suna ganin ko an damka wanda yayi zagin ga hukuma Masu kare hakkin dan Adam zasu shigo ayi ta bugawa wanda hakan zai sa a saki wanda yayi zagin, yaci gaba da rayuwar sa ba tare da daukan matakin na shari’a a kansa ba. “

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button