E/News

Shin Wane ne Marigayi Ebrahim Raisi?

An haife shi a shekarar 1960 a Mashhad inda masallacin ‘yan shi’a mafi tsarki yake, kuma ya bi sawun mahaifinsa ne wanda shi ma malamin addinin musulunci ne.

Ana kallonsa a matsayin wanda zai iya gadon jagoran addinin ƙasar Ayatollah Khamenei, a matsayinsa na mai tsattsauran ra’ayin siyasa.

Ya bi sawun masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Shah wacce aka kifar a shekarar 1979.

Raisi, mai shekara 63, ya zama mataimakin mai shigar da ƙara a Tehran a lokacin yana da shekara 25.

Raisi ya bai wa masu hasashe mamaki a lokacin da ya tsaya takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2017, inda ya zo na biyu a zaɓen.

A shekarar 2019, jagoran addinin ƙasar, Ayatollah Khamenei ya bayyana sunansa a matsayin wanda zai jagoranci ɓangaren shari’ar ƙasar.

A watan Yunin 2021 ne aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasar inda ya maye gurbin Hassan Rouhani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button