Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Najeriya, Nafdac, ta ce za a iya cin taliyar indomie a ƙasar saboda ba ta ɗauke da sinadarin haddasa cutar kansa.
Shugabar hukumar Nafdac, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana haka yayin tattaunawa da wakilin mu, inda ta ce taliyar ta indomie da ta sahhale a ci, a ƙasar ake samar da ita.
Farfesa Adeyeye ta ce a shekarun baya, gwamnatin tarayya ta haramta shigo da indomie cikin ƙasar domin karfafa gwiwar masu samar da ita a ƙasar.
An yi ta samun rahotanni mabanbanta cewa taliyar indomie mai ɗanɗanon kaza da Taiwan da Malaysia ke samarwa, tana ɗauke da sinadarin Ethylene Oxide da ke haddasa cutar kansa.
Sai dai, Nafdac ta ce indomie da ake samarwa a cikin ƙasar ba ta da wata alaƙa da ta Taiwan da kuma Malaysia.
Nafdac ta ce ta fara gudanar da bincike kan taliyar kamfanin Indomie da kuma cikin kasuwannin Najeriya.
Wannan na zuwa ne bayan da Taiwan da Malaysia suka ce wata taliya mai ɗanɗanon kaza na ɗauke da sinadarin da zai iya janyo cutar kansa.
Nafdac ta ce babu irin nau’in taliyar ta indomie a cikin kasuwannin Najeriya, inda ta ce za su yi gwaji don gano ko wasu ɓata-gari sun shigo da ita cikin ƙasar.
Farfesa Adeyeye ta ce taliyar indomie na cikin abubuwan da hukumar kwastam ta haramta shigo da su ƙasar.
Batun sinadari mai jawo cutar kansa da aka ruwaito cewa indomie na ɗauke da shi ya janyo fargaba kan ingancin abinci a duniya ciki har da Najeriya ganin cewa indomie na cikin abubuwan da ake ci kodayaushe a ƙasar.