News

Shikenan Ta tabbatar Siyasar Ganduje Tazo Karshe

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi wata ganawa da zaɓaɓɓen shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu a birnin Paris.

Bayanai sun nuna cewa mutanen biyu sun shafe sa’o’i da dama suna tattaunawar.

Wata majiya da ba ta son a ambace ta, ta tabbatar wa BBC da ganawa a ƙasar Faransa.

Kwankwaso, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Kano ya zo na huɗu a cikin ƴan takarar shugaban ƙasa na 2023, inda ya samu ƙuri’u 1,496,687.

Duk da cewa babu cikakken bayani kan abin da tattaunawar ta ƙunsa, amma ana ganin cewa ba za ta rasa nasaba da shirye-shiryen kafa sabuwar gwamnati da za a rantsar a ranar 29 ga watan Mayu ba.

Bola Tinubu, wanda tsohon gwamnan jihar Legas ne kuma ɗaya daga cikin waɗanda ake wa kallon ƙwararru a siyasar Najeriya, har yanzu bai yi bayani dalla-dalla kan yadda gwamnatinsa za ta kasance ba.

A halin da ake ciki, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Tinubu na ƙoƙari ne wajen ganin ya shirya yadda zai karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayu.

A ranar Laraba 10 ga watan Mayu ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya bayyana cewa zai tafi wata ziyarar aiki a ƙasashen Turai.

Wata sanarwa da ofishin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya fitar, na cewa Tinubu zai yi amfani da bulaguron domin lura da shirye-shiryen miƙa mulki da tsare-tsarensa, ba tare da fuskantar damuwa da yawan ɗauke hankali ba.

”A yayin ziyarar, zaɓaɓɓen shugaban ƙasar zai gana da masu zuba jari da manyan abokan hulɗar kasuwanci domin samar da damar zuba jari a ƙasar ƙarƙashin mulkinsa da aka shirya sabbin tsare-tsaren kasuwanci”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Gabanin tafiyar tasa, Tinubu ya gana da Hon. Tajudeen Abbas da Hon. Benjamin Kalu waɗanda jam’iyyar APC ke mara wa baya domin zama kakakin majalisar wakilan ƙasar da mataimakinsa.

Zaɓen shugabannin Majalisar Dokokin Najeriyar na daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a ƙasar cikin ‘yan kwanakin nan.

Duk da cewa jam’iyyar APC ce ke da mafi yawan sanatoci, amma jam’iyyun adawa sun samu kaso mai yawa, wanda ake ganin zai iya zama barazana ga duk wani yunƙuri na jam’iyyar wajen yin gaban kanta a lokacin zaɓen shugabannin zaurukan majalisar biyu.

Jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso tana da zaɓaɓɓun sanatoci biyu ne da kuma mambobin majalisar wakilan tarayya 19.

Sai dai, ana ganin cewa Rabi’u Kwankwaso na da ƙarfin tasiri sosai a siyasar Najeriya, musamman ma arewacin ƙasar da kuma jihar Kano, wadda ita ce ta biyu a yawan masu kaɗa ƙuri’a a faɗin ƙasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button