Politics

Sheikh Assufiyu Ya Mayarwa Mataimakin Dan Takaran Shugaban Kasa Kashim Shettima Martani

Sheikh Assufiyu Ya Mayarwa Mataimakin Dan Takaran Shugaban Kasa Kashim Shettima Martani

Shugaban Kungiyar Malamai Masana ilimin alkaluma ta ƙasa Sheikh Habibi Abdallah Assufiyu ya mayarwa Mataimakin dan Takaran Shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, martani, akan maganar da ya bayyana a jiya cewa” Baya zamo mataimakin Ahmad Bola Tinubu be domin ya kare martaban musulunci da Musulmai bane.

“Shehin malamin ya bayyana cewa” Kishin addini shine nagartar farko atare da dukkan Shugaba wajen a Al’umma, Shugaban yatabbatar da cewa ajiya Mataimakin dan Takaran Shugaban kasa kuma tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima ya bayyana abunda ke ransa a wata hira da akayi dashi a Channel tv inda yace” basu zo domin sukare martabar addinai ba hasali ma hakan nauyi ne kadai akan mai girma sarkin musulmi naya kare martabar musulmai da musulunci “.

Assufiyu ya kara da cewa” Addini yana nufin shiriya musamman na Islama, kuma addini shine abu mafi girman daraja da muhimmanci awajen kowacce al’umma, da wannan yazama wajibi acikin kalaman dukkan shugaba yazama mai kiyayewa akan abunda yashafi wannan bangare, kuma aduk alkarya akanyi alfahari da samun shugabanni masu kishin addinin su, saboda duk mutumin da babu addini atare dashi babu shiriya atare dashi kwarai, domin baza’a ce yanada dalilin rayuwa adoran kasa ba, saboda haka bai kamata neman kuri’un al’umma ya sanya kalamanka su fitar dakai daga sahun masu kishin addinin ka ba.

A matsayinka na musulmi wanda addini ya koyar dashi muhimmancin martaba da daraja addini, irin kalar wannan furuci na kadaita ko alakanta hakkin kare martaban addini zuwa kan mutum daya ko shugabanni abangaren addinai yakamata yazama abun korewa awajenka, kuma duk shugaba yazama abune mai kyau ya maida hankali wajen ganin addinin kowa a kasar sa ya barranta daga shiga hurumin da bana nasa ba domin a zauna lafiya, domin hakan shima kiyayewa martabar addinai ne ga shugaba.

Kuma da kalar wannan kudiri naku mai nuni da rashin kishin addini afili kuke so al’umma mu mara maku baya domin shugabantar mu ? Babu shakka a daidai wannan gabar zamu ce ba muyi mamakin jin wannan kalar batu daga gareku ba, domin wannan shiri na musulmai biyu a tikiti daya da kukayi a siyasar ku, ba kunyi domin kawo cigaba da gyara bane, face kunaso ku cimma burinku nasamun mulki ne tare da kara bude kofar tsiyataku atsakanin mutane, saboda koda a manufofin ku na neman wannan matsayi bamuji batun hadin kan al’umma ba.

Ya kamata mu al’umma musani cewa duk mutumin da yake ikirarin bazai kare addinin sa ba, da sannu zai banzatar da sha’anin addinin wasu, kuma wannan kadai ya isa ya samar da kofar magana akan fifiko koda nasa bangaren baisamu kulawar da ake zato ba. A kasar nan bama dukkan addinai muhimmanci da kariya a shugabance amatsayinka na dan siyasa ayayinda kazama shugaba shine babban abunda zai baka damar hada kan al’umma har zaman lafiya ya wanzu a kasa.

Mutane masu kalar fahimta da tunani irin na wannan bawan Allah ba abun la’akari bane a fagen siyasa balle a shugabanci a matakin akasa musamman a kasa irin Nigeria, mutanen da addinin su ma baida tabbacin samun kariya daga garesu gwargwadon iko taya zasu maida hankali akan abunda zai baiwa al’umma natsuwa domin gudanar da bauta a addinin su.

Shugaban yayi kira da cewa ” Ya zama wajibi al’umma mu lura da ingancin addini tare da duk mai neman shugabanci a kasar nan, a kowanne mataki domin samun shugabanci na adalci da dacewa kamar yadda galibi addini ne ke saita bawa zuwa ga tsoron Allah da kyawawan ayyuka.

Wannan bawan Allah ba abun duba bane a fagen siyasa balle shugabanci a matakin akasa musamman a kasa irin Nigeria, mutanen da addinin su ma baida tabbacin samun kariya daga gare su gwargwadon iko taya za’a maida hankali akan abunda zai basu natsuwa domin gudanar da bauta a addinin nasu.

Allah yasa mu dace. Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button