Shatu Garko Sarauniyar Kyau. Wannan tsohuwa da ake gani sunanta Grace Atinuke Oyelude, a shekarar 1957 itace mace ta farko Da Ta Fara Zama Sarauniyar Kyau.
DUNIYA TA ISHI MAI HANKALI WA’AZI DAGA DATTI ASSALAFY
Wannan tsohuwa da ake gani sunanta Grace Atinuke Oyelude, a shekarar 1957 itace mace ta farko a tarihin Nigeria da ta fara zama Sarauniyar Kyawawa a gasar al’adun Yehudu, lokacin ma Nigeria bata samu ‘yancin kai ba
Yanzu Grace tana da shekaru 90 a duniya, ta tsufa, yayinta ya wuce, ba wanda yake maganarta balle a kulata, babu masu kula da ita sai jikokinta idan tana da su, talle a manyan kamfanoni kuwa ko tallen goro babu wanda zai bata a matsayin Sarauniyar kyawawa
Kar mu manta, mutanen da suka gabata sun fi na yanzu karko da lafiya da nisan kwana a duniya, amma wannan bai hanasu tsufa ba, bai hana duniya ta sallame daga yayi ko tashe ba, kamar yadda duniya ta sallami Grace ba’a ko labarinta hakanan duniya zata sallami Shatu Garko wanda wakilan Yehudawa suka bata kambi a yanzu
Gashi mutanen yanzu ba ma jimawa ake a duniyar ba, babu karko, ba isasshen lafiya, ga shafe shafen chemicals na mayukan bleaching da suke illata karfin fatar jiki, masu bleaching suna dena shafa mayukan bleaching na wata daya zaka gansu kamar karaciyan jeji sun zama two colour suna waari, lokacin da zasu rasa kudin sayan mayukan bleaching yana tafe da wuri indai duniya ne
Duk wani abin sharri da za’a kawo sai a hada da mata, muna jan hankalin iyaye musamman ‘yan mata Musulmai, ku barwa yahudawa tarkacensu, kar kwadayin abin duniya yasa ku rudu da al’adun Yehudu, kuyi fatan Allah Ya baku mazan kwarai kuyi aure yafi zama alheri a gareku
Muna rokon Allah Ya tsare mana imanin mu a har kullun, Daga Datti Assalafy