Uncategorized

Sannu A Hankali Allah Ya Na Fito Da Malamai Cikin Malaman Arewa Dake bada Muguwar Fatawa Ta Hanyar Cin Amanar ilmi- Datti Assalafy

Sannu A Hankali Allah Ya Na Fito Da Malamai Cikin Malaman Arewa Dake bada Muguwar Fatawa Ta Hanyar Cin Amanar ilm

Sannu a hankali Allah Ya na fito da wasu irin Malamai a cikin Musulmin Arewacin Nigeria wadanda suke bada muguwar fatawa ta hanyar cin amanar ilmi domin su farantawa Yahudu da Nasara rai, da neman yardan gungun mutane ‘yan duniya

Ga wani Malami nan daga Jihar Kano wanda shine shugaban majalisar kungiyar Malamai na kasa reshen jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil yayi hira da babbar kafar yada labarai na yahudawan Kasar Ingila wato BBC inda Malamin ya fito ya halalta sauraran wakoki da kade-kade da kuma karta

Na saurari hiran da kafar yada labarun yahuu BBC sukayi da Malamin tun daga farko har karshe a inda ya halalta kida da wakoki da karta, ya kawo dalilai daga cikin binciken kimiyyar zamani na Turawa ya bayyana amfanin sauraran kida da waka

To amma masu karin magana sunce ba’a yin karyaa a kusa da gida, kasa da kwana daya da wannan Malamin ya bada fatawar karyaa da haa’inci, babban Malamin Musulunci Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Lemo ya buga masa kusa inchi 12 a tsakar kansa, inda ya dirkake Malamin da ruwan dalilai daga Qur’ani da Hadisi ya rusa fatawarsa na karyaa da haa’inci

Ya kamata BBC suyi check and balance su saka fatawar Dr Muhammad Sani akan haramcin waka da kida, to amma da yake tashace ta yahudawa, kuma manufarsu kenan su gurbaata kwakwalwan Musulmai ba zasu saka fatawar Dr Muhammad Sani ba

Sheikh Dr Muhammad Sani ya banbace tsakanin waka da kida da kuma wake (nasheed) ya yiwa Ibrahim Khalil raddi na ilimi kuma ya ba shi kyautar ilimi, Malam ya ce Annabi (SAW) ko Sahabbai basu taba yin waka da kade-kade ba, sannan ya kawo ayoyi da maganganun Malamai akan fatawar yin waka

Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Ilmi yaja hankalin Ibrahim Khalil akan ya ji tsoron Allah ya dena cakuda abubuwa don jahilai su tafa masa, kuma ya bashi shawara idan bashi da ilimi a kan abu to ya dena kokarin kawo wa mutane rudu a cikin addini

Muna rokon Allah Ya ja kwana Sheikh Dr Muhammad Sani Rijiyar Ilmi, Allah Ya shiryar mana da Malamai ‘yan duniya, Ya kare Musulunci da Musulmai daga kaidinsu Amin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button