News

Ran Amaechi ya ɓaci bisa rashin saurin aikin jirgin ƙasa na Kaduna-Kano da Port Harcourt-Maiduguri

Ran Amaechi ya ɓaci bisa rashin saurin aikin jirgin ƙasa na Kaduna-Kano da Port Harcourt-Maiduguri

Ministan harkokin Sufuri, Rotimi Amaechi, ya nuna ɓacin ransa ga Kamfanin Fasahar Gine-gine na China, CCECC bisa yadda aikin layin dogo na Kaduna-Kano ya ke tafiyar wahainiya.

Amaechi ya baiyana ɓacin ran nasa ne a yayin ziyarar duba yadda aikin ke tafiya da kuma na Tashar Sauke Kayayyaki ta Dala, wato ‘Dala Dry Port’s tare da wasu masu ruwa da tsaki a jiya Asabar a Kano.

A cewar Amaechi, aikin ba ya sauri kwata-kwata, inda ya ƙara da cewa kayan aiki 2000 ya kamata a kawo, amma an ɓuge da kawo guda 541.

“Sun ce sun kai kayan aiki sama da 300 a Kaduna kuma an tafi anje a tabbatar. To in ma hakan ne, ya zama 800 kenan idan a ka kwatanta da 2000 da ya kamata a kawo. Sabo da haka akwai matsala,” in ji shi.

Haka-zalika Ministan ya nuna rashin jin daɗin bisa yadda CCECC ɗin ko fara aikin tashar ma ba su yi ba.

Ya ƙara da cewa kamata ya yi a ce CCECC sun yi wa Ma’aikatar sa bayani sabo da an riga an basu wasu da ga cikin kuɗaɗen da za a basu, inda ya ce ya kamata a ce an an fara aiki a wajen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button