News

Naga Shekau Da Ido Na Bai Mutu Ba, Kuma Akwai Yan Matan Chibok Har Yanzu A Wajen Boko Haram- Mariam

Naga Shekau Da Ido Na Bai Mutu Ba, Kuma Akwai Yan Matan Chibok Har Yanzu A Wajen Boko Haram- Mariam

Shekaru takwas bayan da mayakan Boko Haram suka sace ‘yan mata 276 a makarantar Sakandaren ‘yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno, rundunar jami’an soji ta Operation Hadin Kai ta ceto wasu ‘yan matan Chibok biyu a dajin Sambisa.

An bayyana cewa an kubutar da su ne a yankin Gazuwa da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno a kwanakin baya.

An kubutar da Mariam Dauda da Hauwa Joseph ne tare da jariransu a lokacin da suke ba da labarin abin da ya faru na tsawon shekaru 8 da suka yi a cikin dajin a wani taron manema labarai da aka gudanar a babban dakin taro na Command-and-Control Center Maimalari da ke Maiduguri a ranar Talata.

Sun bayyana cewa an daura musu aure da Kwamandojin Boko Haram tsawon shekaru kuma dukkansu sun haifa musu jarirai.

Wadanda suka tsira sun ci gaba da cewa sojojin Najeriya sun kashe mazajensu watanni da suka gabata.

Yayin da take amsa tambayoyin manema labarai, Maryam a yanzu ta ce, “Eh na san shi, na taba ganin marigayi Abubakar Shehau.

Ta ci gaba da cewa, “Eh, har yanzu akwai sauran ‘yan matan Chibok a dajin Sambisa.

Suma sun yi aure, akalla sama da 20 suna nan.” Ta fara ambaton sunayensu daya bayan daya.

Kwamandan rundunar Manjo Janar Christopher Musa, ya ce an samu nasarar ne sakamakon gagarumin farmakin da sojoji suka kai a dajin Sambisa, da tsaunin Mandara, da yankin tafkin Chadi.

Musa ya lurar da cewa an ceto ‘yan matan a Sambisa yayin da ya tabbatar da cewa ba za su huta ba har sai sauran wadanda aka sace sun samu ‘yanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button