Mun kama matasa 78 bisa zargin aikata baɗala ne ba auren jinsi ba — Hisbah
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce matasa 78 da ta kama ba bikin auren jinsi su ka je yi ba, sun dai je bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ƙawar su ne, shi ne su ka ɓige da aikata baɗala.
A yau Laraba ne dai BBC Hausa ta rawaito cewa Hukumar Hisbah a Kano ta kama mutum 78 maza da mata bisa zargin za su yi auren jinsi.
BBC ta ƙara da cewa an kama su ne a Unguwar Nasarawa GRA a wani gida da ake kira White House.
Amma, da Daily Nigerian Hausa ta tambaye shi kan sahihancin labarin, Nasiru Isa, Mataimakin Kwamandan Hisbah ɓangaren Sintiri, ya kore rahoton na BBC, in da ya ce ba auren jinsi a ke yi a wajen da a ka kama matasan ba.
A cewar sa, hukumar ta samu rahoton cewa maza da mata ne su ka taru domin bikin murnar zagayowar ranar haihuwar ɗaya da ga cikin su.
Isa ya ƙara da cewa Hukumar ta samu bayanin sirri cewa matasan sun je gurin ne da kayan shaye-shaye kuma su na ta aikata baɗala, shi ne a ka aika jami’ai domin su daƙile bikin su kuma kamo masu aikata laifin.
Mataimakin Kwamandan ya ce tuni hukumar ta yi wa matasan wa’azi ta kuma kira iyayen su domin su ga abinda ƴaƴansu su ke yi.
Ya kuma yi kira ga iyaye da su kula da ƴaƴansu da kyau domin mafi yawa da ga cikin yaran da a ka kama, ƙarya su ka yi wa iyayen na su cewa za su je ziyara ko kuma kai ɗinki da sauran su.
“Anyi musu wa’azi. An musu nasiha kuma an gaiyato iyayensu domin susan abinda yaran su ke yi. Da yawa sun yaudari iyayeyan su ne ,kuma mai girma Kwamanda ya bada umarni a mikasu zuwa ga iyayen su,”
Da wakilin mu ya tambaye shi gaskiyar rahoton cewa an samu kwaroron roba da dama a wajen bikin, Isa ya ce wannan rahoton ba gaskiya ba ne.
Ya kuma ce Hukumar Hisbah ba za ta riƙa zura ido a na aikata saɓon Allah ba, inda ya jaddada cewa ba za su gajiya wajen umarni da kyakkyawan aiki da hani da mummuna ba a ciki da wajen birnin Kano.