Masu garkuwa sun bukaci babura da kayan abinci a matsayin fansa a Kaduna
Masu garkuwa sun bukaci babura da kayan abinci a matsayin fansa a…
Wadanda suka yi garkuwa da mutum 14 a kauyen Janjala da ke Karamar Hukumar Kagarkon Jihar Kaduna sun bukaci ’yan uwan wadanda suka sace su kai musu sabbin babura guda biyu da kayan abinci a matsayin fansa.
Sun kuma bukaci a hada musu da kwayoyi da kuma barasa matukar ana so su saki mutanen.
Aminiya ta rawaito cewa maharan sun sako uku daga cikin mutanen da suka sace a kauyen Kadara da ke makwabtaka da Janjalar, bayan sun karbi kayan abinci da kwayoyi, a madadin sabbin kudin da suka ki karba tun da farko.
Da yake zantawa da wakilinmu ta wayar salula a ranar Lahadi, Sakataren Dagacin Janjala, Babangida Usman, ya ce masu garkuwar sun ce musu tun da samun sabbin kudaden na Naira miliyan 14 ya yi wahala, a samo musu baburan da kayan abinci.
“Halin da ’yan uwan mutanen suke ciki ke nan. Yanzu kuma yadda za a sami kudin da za a sayi wadannan kayayyakin ita ce babbar matsala,” in ji Babangida.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ba ta magantu ba a kan lamarin