News

Masha Allah: Kyakkyawan Shiri Akan Kashe Makudan Kudade A Harkar Aure A Jihar Sokoto

Mahukunta a Najeriya cikin sauran wa’adin da ya rage musu akan mulki sun ci gaba da yunkurin samar da hanyoyin da za su iya saukaka lamurran rayuwa da kuma kare martabar al’umma musamman marasa karfi .

La’akari Da yadda wasu al’adu ko dabi’un al’umma a wasu yankunan Najeriya suke kara kawo matsin a rayuwa musamman ga marasa karfi daga cikin al’umma, gwamnatin jihar Sokoto take kokarin haramta yin almubazzaranci a lokacin bukukuwa.

Daga cikin al’adun sun hada da wadanda ake samu a lokutan bukukuwa musamman wadanda suka shafi aure, bukin suna da makamantan su a arewacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar dokokin jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya ta amince da dokar hana almubazzaranci a lokacin bukukuwa.

Hakan yasa da yawa jama’a na kokawa akan illolin da yin almubazzarancin a lokutan bukukuwan ke haifarwa a cikin al’umma.

Al’ummar jihar Sakkwato ta shiga sahun wasu al’ummomi da suka yunkara don kawo sauyi ga wadannan al’adun ta yadda jama’a zasu rika samun sauki.

Dan majalisar jiha mai wakiltar mazabar Yabo wanda kuma shine shugaban kwamitin lamurran addini a majalisar Abubakar Shamaki Yabo shi ya jagoranci gabatar wa majalisar, wani kudurin doka akan hana almubazzarancin a lokutan bukukuwan.

Dan majalisar yace bisa ga korafe-korafe da suke samu daga jama’a akan illolin almubazzarancin ne yasa dashi da abokin aikin sa dun ga ya dace a sake yin gyara ga dokar ayi ma kwaskwarima ta dace da yanayin da ake ciki yanzu.

Dokar dai ta kayyade abubuwan da za’a rika bayarwa a lokutan neman aure da wasu bukukuwa.

Acewar dan majalisar Sadaki zai kasance kwatankwacin darajar daya bisa hudu na kudin dinari Kamar yadda Musulunci ya amince, kayan neman aure kuwa ba zasu wuce kwandon goro biyu ba, da kwalin alawa biyu da kudi naira dubu ashirin, kayan lefe ma kar wuce turamin atampa goma.

Duk da yake gwamnatin Sakkwato bata kai ga sa hannu ga dokar ba kafin ta soma aiki masana na ganin wannan tsarin zai yi tasiri.

Almubazzaranci a lokutan bukukuwa dai ya jima yana ci wa ‘yan Najeriya tuwo a kwarya, abinda ya kai aka samar da dokokin takaita matsalolin a wasu jihohi kamar kano da Jigawa, har a yankin kudancin Najeriya a wasu jihohi an hada almubazzarancin bukukuwan jana’izar mamata da wasu bukukuwa.

Saurari rahoton Muhammad Nasir:

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button