Babban mai shigar da ƙara na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ya nemi kotun ta ba da umarnin kama Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da kuma jagoran Hamas a Gaza saboda aikata laifukan yaƙi.
Karim Khan ya ce akwai hujjoji ƙarara da ke tabbatar da cewa ɓangarorin biyu sun aikata laifukan yaƙi da na tarwatsa rayuwar ɗan’adam daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Kotun ta ICC da ke birnin Hague na bincikar ayyukan Isra’ila a yankunan Falasiɗnawa da ta mamaye tun daga shekara uku da suka wuce – da kuma ayyukan Hamas a baya-bayan nan.
Mista Netanyahu ya siffanta ba da umarnin kama shugabannin Isra’ila da ICC za ta yi a matsayin “abin takaici da zai jawo matsala a tsawon tarihi”.