News

Kotu Ta Tura Nana Hauwa Gidan Gyaran Hali A Sakkwato

Kotu Ta Tura Nana Hauwa Gidan Gyaran Hali A Sakkwato

Babbar Kotun Jihar Sakkwato da ke karkashin Mai Shari’a Mohammed Mohammed, ta daure wasu mutane biyu namiji da mace da ke damfarar mutane a na’urar cire kudi na Banki (ATM).

An tuhume su ne da laifin hada baki wajen aikata laifi da kima sata, yayin da Hukumar EFCC ta yankin Sakkwato ta gabatar da shaidun da ke tabbatar da laifin da aka tuhume su da akatawa.

Kotun ta daure Abdulmajeed Habeeblah da Nana Hauwau Umar shekara uku a gidan kurkuku kowannensu bayan ta same su da laifin damfarar jama’a a na’urar cire kudi ta Banki (ATM).

Kotun ta yanke masu hukunci ne ranar Litinin nan da ta gabata, bayan ta gama gamsuwa da shaidun da Hukumar EFCC ta gabatar mata.

Wadanda aka gurfanar din sun amsa laifuka guda biyu da aka tuhume su da akatawa. Ganin ba su wahalar da shari’a ba, sai kotun ta yi masu sassauci, ta daure su shekara uku kowannensu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button