News

Kasar Nijar Ta Karrama Gwamna Matawalle Na Jihar Zamfara Da Lambar Yabo Kan Kokarinsa Na Kawo Karshen Matsalar Tsaron Da Ya Addabi Yankunan Arewa

Kasar Nijar Ta Karrama Gwamna Matawalle Na Jihar Zamfara Da Lambar Yabo Kan Kokarinsa Na Kawo Karshen Matsalar Tsaron Da Ya Addabi Yankunan Arewa

Daga Isah Abdullahi Dankane

Gwamnan ya karbi wannan lambar yabon a hannun shugaban kasar Muhammad Bazoum.

A wurun bikin cikar kasar ta Nijar shekara 62 da samun ‘yancin kai daga Turawan Faransa a yau Talata.

Bikin ya gudana ne a birnin Tillabery da ke yankin yammacin kasar wanda yake iyaka da kasashen Mali da Burkina Faso masu fama da rikicin ta’addanci.

Shugaba Bazoum ya ce jamhuriyar Nijar ta karrama Gwamna Matawalle ne saboda irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasa da ta’addanci wanda ya taimaka matuka wajen tabbatar da tsaron kasar da makwaftan jihohin Arewa maso yammacin Najeriya.

Hakika Gwamna Matawalle yana matukar kokari akan matsalar rashin tsaron da ya addabi jihar Zamfara dama yankin Arewa, Fatanmu Allah ya kara dafa mishi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button