Karya kukeyi Kasar Amurka Bata Saka Sunan Pantami Acikin Jerin Masu Daukar Nauyin Ta’addanci A Nigeria ba Inji Mai Taimakawa Shugaban Kasa Kan Kafofin Yada Labarai Bashir Ahmad.
A wani labari da ya karade kafofin Sada zumunta Wanda jaridar NewWireNGR ta rawaito cewa.
Kasar amurka na zargin ministan sadarwa da Tattali Dr. Ali Isa Pamtami da taimakawa ta’addanci a nigeria.
Lamarin da ya haifar da cece kuce a shafukan sada zumunta tare da dasa ayar tambaya ga dubban yan nigeria.
Wanda akasari masu karatu ke kokwanto ga sahihancin labarin.
Sai dai a wani rubutu da mai taimakawa shugaban kasa Muhammadu buhari kan kafofin sada zumunta wato bashir Ahmad ya wallafa a shafinsa na twitter cewa.
Cikin Sauri kun amince da rahoton karya ba tare da Kun tabbatar ba. A matsayinku na kafar yada labarai @NewsWireNGR Yakamata Ku san hakikanin yadda ake tantance irin wadannan rahotannin, amma a’a, Kawai Kunzo Kuna tura labarin karya wanda ke cike da hadari ga dubban mabiyan ku. FYI @DrIsaPantami bai kasance cikin kowane jerin sa’ido na Kasar Amurka ba.
Tuni dai yan nigeria suka shiga tofa albarkacin bakin su ga wannan labari.
Yayin da wasu ke karyatawa a gefe guda kuma wasu na tambayar mai yasa shi Dr Isa Ali Pamtami bai fito ya karyata rahoton dakamsa ba.
Anan mukeso daku bayyana mana ra’ayinku game da waannan rahoto
Follow Us
Back to top button