Kalubale Dakuma Nasarar Da Nijar Zata Fuskanta Bayan Ficewa Daga Kungiyar ECOWAS
Wane Alfanu ko matsaloli ke cikin fita ECOWAS?
Masu cewa babu matsala don an fita ba su san girman ECOWAS da tasirinta a ƙasashen ba ne. Akwai yarjeniyoyi da dama, musamman ɓangaren kasuwanci, da tafiye-tafiye da al’ummomin waɗannan ƙasashen ke amfana da su.
Idan aka ce yau sun fita to wataƙil komi zai sauya, sai dai in sun sake wasu yarjeniyoyi tsakaninsu.
Sannan waɗannan ƙasashen kuɗi ɗaya su ke anfani dashi, banki ɗaya. Kuma duk ƙasar da su ka sanyawa takunkumi to za a kulle kuɗaɗen tane.
Ba zata iya amfani dasu ba. (Yanzu hak Nijer tana da maƙudan kuɗaɗe amma ba ta iya amfani da su saboda takunkumin) to amma yanzu sun fita dole su nemi hanyar da za su iya amfani da kuɗaɗen su. Ko kuma su ɗau mataki na Shari’a.
Sannan akwai batu na zirga-zirga, a ƙasashe musamman mutanenmu na Nijer da ko ina a nan Afrika su ne.
Ta yu ƙasar da ka ke, ko ka ke son zuwa; in dai mamba ce, a ECOWAS to duk ɗan wata ƙasa ECOWAS ya kan samu rangwame, ko sauƙi.
Ko kuma a ce dole zuwa can sai da Fasfo (Passport) ko kuma a ce zama ƙasar sai da wasu takardu, amma wannan duk mai sauƙi ne, saboda ko yanzu da ECOWAS ɗin, kowace ƙasa za ka je kana da Fasfo baka da ita, sai ka biya kafin ka wuce ko da fasfon ECOWAS ɗin gareka.
Wasu ma duk shekara sai kun yi takardun zaman ƙasa. Shi yasa bata da amfani kungiyar.
Sannan abo na gaba, waɗannan ƙasashe sun kama hanya ta samun cikakken inci, wanda basu cikin wata kungiya, wadda ƙasashen yamma Irin su Faransa Amurika ke juyata, ke nan karkashin wannan kowace za ta iya ƙoƙari ta nemi hanya da zata iya dogara da kanta, da yin tsari na shugabanci nagari, wanda zai kai ga ƙasar gaba. wanda zai kai har ƙirƙirar kuɗinta na kanta.
Amma fa wannan ba abo ne mai sauƙi ba, ko an yi akwai kalubale. Ko dai ma, menene wannan abo matuƙar nan gaba ba a saka siyasa ba, aka ɗore kuma aka yi haƙuri da ƙalubale da wahalhalu, kuma su ka yi ƙoƙarin kawo gyara, to wallahi nan gaba za a ji daɗi, amma fa sai an yi haƙuri.
Don wannan Tsarin ba zai yiwa, manyan kasashe daɗi ba, kuma dole su ɗau mataki na ruguza shi.
Allah ya kyauta ya kawo mana sauƙi Amin
Abuzaid ɗan Nijer 🇳🇪✍️.