News

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un;! Bidiyon Ambaliyar Ruwan Da Ta Hallaka Mutum Sama Da 100 A Nijar

Innalillahi wa inna ilaihir raju’un;! Bidiyon Ambaliyar Ruwan Da Ta Hallaka Mutum Sama Da 100 A Nijar

Ambaliyar ruwan da ake fuskanta a sassan Nijer sanadiyar ruwan saman da ake yi ta haddasa asarar rayukan mutane fiye da 100 sannan ta yi sanadin hasarar dimbin dukiyoyi, lamarin da ya sa gwamnatin Nijer soma neman gudummowar abokan hulda na kasa da kasa don agaza wa wadanda bala’in ya rutsa da su.

NIAMEY, NIGER – A taron manema labaran da ya kira ranar Alhamis, ministan ayyukan jinkai na Nijer Alhaji Laouan Magaji, ya yi bitar halin da ake ciki a fadin kasar sakamakon ruwan saman da aka tafka daga watannin Yuli da Agusta zuwa ranar 13 ga watan nan na Satumba.

Ya ce a duk jihohin kasar 8 ruwa yayi gyara/barna, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 137 dubban wasu kuma suka rasa matsugunnansu. Hakazalika dabbobi da dama sun mutu.

Ministan ya ce gwamnati ta samar da agajin gaggawa ga mutunen da wannan bala’in ya afkawa da dan abinda ba za a rasa ba, a saboda haka ya bukaci gudummowar kasashe da kungiyoyi masu hannu da shuni.

A yankunan da wannan al’amari ya fi muni, ambaliyar ta tilasta wa dimbin mutane tserewa zuwa makarantu a wani lokaci da ake shirin komawa ajin karatun shekarar 2022-2023, a saboda haka gwamnati ta umurci magadan gari su dauki matakai kafin zuwan ranar bude makarantu.

Saurari cikakken rahoton Souley Mumuni Barma:

https://youtu.be/80BzNPN3zMQ

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button