Idan Ni Dan Aljannah Ne, A Dauki Aljannah Dina A Ba Abdullahi da Amina — Yusuf Na Dabo
Daga Mujahid Lawal S Jumare
Shahararren mawakin manzon Allah mazaunin Kofan Jatau, Yusuf Nadabo, ya yi tsokaci dangane da muhawarar da ake ta tattaunata a tsakanin musulmai dangane da makomar iyayen manzon Allah (SAW).
Yusuf Na Dabo, ya yi tsokacin ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafin sada zumuntan Facebook yanda ya nunar da rashin muhimmancin tattauna irin wannan kadiyar tare da daukan alkawarin sadaukar da sakamakon Aljannarsa wa iyayen manzon Allah matukar ya kasance shi dan Aljannah ne.
A cewarsa; “idan ni dan aljannah ne, a dauki aljannah dina a ba Abdullahi Da Amina; saboda na tabbatar manzon Allah zai ji dadi ya ga iyayensa a Aljannah” .
Na Dabo, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da yanda wasu su ke fitowa karara su na bayyana cewa iyayen Manzon Allah ba za su shiga Aljannah ba tare da janyo hankulan musulmai da su shiga taitayinsu akan irin wannan zantukan.
Yusuf Na Dabo, ya jaddada cewa Hadithan da aka dogara da su na cewa iyayen manzon Allah ba za su shiga Aljannah ba, babu ko guda daya daya ambaci sunan iyayen manzon Allah a yayin da kuma ya kasa ma su tattauna wannan kadiyyar gida uku.
A cewarsa; “Idan aka dunkule gabadaya cikin ma su magana akan iyayen manzon Allah za ka iya kasasu kashi uku; akwai wa’inda su ka ce suna Aljannah. Akwai wa’inda su ka ce al’amarunsu abarwa Allah. akwai wasu yan kadan, don zan ce yan kadan — da su ka ce iyayen manzon Allah na wuta! Wa iyazubillah!!!”