Kannywood News

Full tarihin rayuwar Murja Ibrahim Kunya tun daga Haihuwar ta, Da Aurenta, har Shigowar ta Cikin Kano.18

Full tarihin rayuwar Murja Ibrahim Kunya tun daga Haihuwar ta, Da Aurenta, har Shigowar ta Cikin Kano.

Tun bayan kamun da hukumar Hizba ta Kano ta yi wa fitacciyar ƴar Tiktok din nan a arewacin Najeriya, Murja Kunya, da kuma gurfanar da ita gaban kotu a inda aka aike da ita gidan gyaran hali, al’amura suke ta faruwa dangane da ita.

Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

Babban batun da ya fi ɗaukar hankalin al’ummar Kano da arewacin Najeriya shi ne yadda aka saki Murjar ta bar gidan gyaran hali, wani abu da ya sa aka yi ta zargin jami’an gwamnatin Kano.

To sai dai gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce sam ba ta da masaniyar yadda Murja ta fice daga gidan gyaran halin, inda mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce “kujerar gwamna ta fi karfin mayar da hankali kan wannan batu”.

Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

Da safiyar Talata ne kuma wata kotu a Kano ta aike da Murjar zuwa asibitin masu larurar kwakwalwa har na tsawon watanni uku domin a “duba lafiyar kwakwalwarta”.

Wannan dai ba shi ne karon farko da hukumar Hisbah ke kama ko gayyatar Murja Kunya bisa tuhume-tuhumen “tsageranci” da yada “badala” a cikin al’umma ba.

Hakan ne ya sa mutane da dama ke dasa ayar tambaya cewa wai wace ce wannan Murja Kunyar da ke yawan janyo ce-ce-ku-ce?

Domin amsa wannan tambaya BBC ta samu tattaunawa da wasu mutanen garin Kunya da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Minjibir a jihar Kano wanda nan ne mahaifar fitacciyar ƴar Tiktok ɗin.

2022
Rayuwar Murja Kunya

An haifi Murja a garin Kunya kimanin shekara 27 zuwa 28 da suka gabata a garin na Kunya.

Murja ƴa ce ga malam Ibrahim da malama Hindatu dukkanin su mazauna garin na Kunya.

KU KALLI BIDIYON TA A KOTU

Murja ba ta halarci makarantar boko ba amma ta yi makarantar Islamiyya ta Fodiyya da ke cikin garin na Kunya.

To sai dai tun kafin Murja ta kammala makarantar Fodiyya din ne mahaifanta suka cire ta aka yi mata aure, inda ta fara auren wani ɗan sanda a garin Minjibir, kafin mutuwar auren inda ta sake auren wani a karo na biyu a garin Gandurwawa duka a ƙarƙashin ƙaramar hukumar ta Minjibir.

Murja Ibrahim Kunya
Murja Ibrahim Kunya

Bayan rabuwa da mijin nata na biyu ne kuma Murja ta koma garin Kunya kafin daga bisani kuma ta bar mahaifar tata zuwa birnin Kano kimanin shekaru 10 da suka gabata.

Harkar siyasa

Murja Kunya na bayyana kanta a matsayin ɗaya daga cikin magoya bayan gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Ta yi suna ƙwarai a matsayin ɗaya daga cikin wadanda suka ba shi goyon baya a lokacin yaƙin neman zaɓe.

A lokuta da dama an ji gwamnan na jihar Kano na ambatar sunanta a wuraren taruka, ciki har da lokacin da aka rantsar da shi a watan Mayun 2023.

Sai dai ana ganin cewa ta goyi bayan Abba Kabir ne bayan taƙaddamar da ta shiga tsakanin ta da gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, wanda a lokacin mulkinsa ne hukumar Hizba ta kama tare da yanke mata hukuncin yin shara a asibitin Murtala da ke Kano na tsawon mako uku ba tare da zaɓin biyan tara ba.

Watch More..

A wancan karo ma an yanke mata hukuncin ne bayan kotu ta same ta da laifin wallafa bidiyon da bai kamata a shafin sada zumunta.

Me al’ummar Kunya ke cewa kan Murja?
Ra’ayoyi sun banbanta dangane da abin da al’ummar garin Kunya ke cewa kan Murja Kunya. Yayin da wasu ke allawadai, wasu kuma na yin san-barka ga fitacciyar ƴar Tiktok ɗin.

Ga abin da wasu jama’a ke cewa kan Murja amma BBC ba za ta kama suna ba:

“Gaskiya Murja ba ta da tarihin tabin hankali amma dai kai kana ganin abin da take yi ka san mutum natsattse mai hankali ba zai yi ba”. In ji wani dan Kunya.

Dangane kuma da abin da ya shafi halayyar Murja wani ya shaida mana cewa “Murja mace ce mai tausayi da taimakon mahaifanta da ƴan’uwanta. Takan shigo duk wata ta yi wa jama’a alheri.

Sannan ba ta manta da al’ummarta ba domin ko ‘hawan dokin kara’ da aka yi a kwanakin baya a nan Kunya ita ma ta yi hawan da tawagarta”. In ji mazaunin na Kunya.

Batun shahara a kafar Tiktok shi ma ya raba kan al’ummar garin inda mutumin da BBC ta tattauna da shi ya ce “gaskiya da dama ba sa jin daɗin irin abubuwan da take yi a Tiktok amma wasu kuma su suna ma ganin kamar wata burgewa ce sannan kuma suna tunanin kamar ta ƙara ɗaukaka sunan garin Kunya.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button