An Kai Wadanda Ake Zargi Da Kisan Dalibar Da Ta Yi Sabo A Sokoto Gidan Gyara Hali
A Najeriya wata kotun majistire dake, Sakkwato ta tura mutanen nan biyu da aka kama da ake tuhuma dangane da kisan daliba Deborah Samuel a gidan gyarar hali.
Sokoto, Nigeria – Rundunar ‘yan sandan Najeriya ce ta kama matasan biyu ranar Alhamis 12 ga watan Mayu, a lokacin da dalibai suka kashe Deborah Samuel kuma suka kona ta akan zargin ta yi batanci ga fiyayyen halitta.
A wannan Litinin 16 ga Mayu ce aka gurfanar da matasan biyu: Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunci, wadanda dalibai ne a kwalejin ta koyar da malanta ta Shehu Shagari.
Sai dai bayan da aka karanta musu laifin da ake tuhumarsu wanda ya yi sanadin salwantar rayuwar Deborah sun ki aminta da laifin abinda ya sa dan sanda mai gabatar da kara, Inspector Khalil Musa, ya nemi kotun da ta kara basu lokaci domin fadadawa da kammala bincikensu.
Jagoran lauyoyi dake tsaya wa wadanda ake ake tuhuma Farfesa Mansur Ibrahim ya aminta da karin lokacin da ‘yan sandan suka nema, kuma ya shigar da wata bukata ta neman bayar da belin wadanda ake tuhuma.
Jagoran lauyoyin ya karanto sashe na 157 da 161 (a’f) da sashe na 164 na dokar aikata manyan laifuka ta jihar Sokoto, da kuma sashe na 35(5) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 mai kwaskwarima a zaman hujjojin neman belin.
Ga Bidiyon Nan Ku Kalla
https://youtu.be/penXf4eYbQQ