News

Fargaba nake kar EFCC ta damke ni, inji Abdul wanda zai tashi da N129.6b idan Pi (π) ta fashe

Fargaba nake kar EFCC ta damke ni, inji Abdul wanda zai tashi da N129.6b idan Pi (π) ta fashe

Abdullahi Abdullahi Ibrahim, dan shekara 18 da ya zage damtse wurin hako Pi (π) ya bayyana fargabar da ya shiga bayan ganin alamar ya kusa zama biloniya a wata zantawa da wakilin Labarun Hausa tayi da shi.

Abdul wanda tela ne sannan kuma dalibi ya bayyana yadda ya fara harkar Pi (π) kusan shekara daya da ta gabata inda yace yanzu haka ya tara Pi 720.

A labarinmu na baya, mun bayyana yadda shugaban Pi na Tudun Wadan Zaria, Abubakar Aminu Maude ya ce, kimar ko wanne Pi daya yanzu haka ta kai N180,000,000.

A yadda mu ka kiyasta, Abdullahi zai tashi da N129,600,000,000 idan har Pi ta fashe a wannan darajar da take a halin yanzu, idan kuwa ta karu, akwai yuwuwar dukiyar Abdul ta zarce hakan.

Ya kuma ba da kaimi wurin ganin cewa ya ci gaba da kara yawan Pi dinshi. Da alamar harkar Pi ita ce hanya mafi sauki da mutum zai tara abin duniya daga kashingide ba tare da yin wani aikin karfi ba.

Ma’abota harkar su na ganin cewa nan gaba kadan mutanen da basu shiga harkar ba za su ciza yatsa, bayan ganin dukiya mai tarin yawa ta samu.

Kuma in har harkar ta fashe, babu shakka zai kasance a ko wanne layi da ke Najeriya akwai biloniya, bisa kiyasin da Labarun Hausa tayi.

Don yanzu haka alkalla cikin kaso 100 na matasa, kaso 40 sun shiga harkar dumu-dumu.

Yanzu haka kimar duk Pi (π) daya ya kai N180m, cewar shugaban ‘yan Pi na Tudun wadan Zaria
Yayin da matasa da dama su ka bazama su na shiga harkar Pi (π), inda su ke kyautata zaton harka ce ta samun dukiya mai tarin yawa a saukake ta wayoyinsu ba tare da yin wani aiki karfi ko kuma zuwa wani wuri ba, Jaridar Labarun Hausa ta samu nasarar tattaunawa da shugaban ‘yan Pi na Tudun Wadan Zaria mai suna Abubakar Aminu Maude, wanda ya feda mana daga biri har wutsiyarsa dangane da harkar.

Da farko ya fara bayyana sunansa tare da yadda ya tsinci kansa a cikin wannan harka ta tara kudi a saukake kuma daga kwance. Ya ce ya dade yana jin labarin Pi, amma bai dauke shi da muhimmanci ba, yanzu kuwa da ya bincika kuma ya samu karin bayani dangane da harkar, ya yarda tabbas gaskiya ce.

A cewarsa, yanzu haka ya kai shekara daya da fara harkar kuma ya tara Pi fiye da dubu daya da dari biyarwadanda yake da ran nan ba da jimawa ba zai mori tagomashinsu. Abubakar ya ce da wayar salularsa ya samu manhajar wacce ba tare da ya sanya ko sisi ba ya fara tara abin duniya.

Ta hanyarsa akwai mutane da dama da su ka fara, kuma yanzu haka su kansu sun fara ganin irin yawan dukiyar da su ka tara a harkar. Yayin da wakilin Labarun Hausa ya tambayeshi ko akwai kasashen da su ka fara amfani da Pi, sai ya kada baki yace:

“Eh tabbas, akwai kasashen da su ka fara amfani da Pi wurin siyayyar abubuwa da dama. Kamar China da Indonesia, duk sun fara harkar. Yanzu haka ana sa ran nan ba da jimawa ba kowa zai yarda da Pi, kuma ya samu karbuwa a duniya.”

Bayan tambayarsa kimar ko wanne Pi daya a kudin Najeriya, ya bayyana cewa:

“Eh to, a yanzu dai babu inda aka tsayar da kimarsa. Sai dai ba Naira ba, ko dala, Pi ya fi su daraja. Don a kiyasin da ake yi yanzu haka, ko wanne Pi daya yana daidai da $314,159, wanda yayi daidai da N180,000,000 da ‘yan kai.”

Kuma a cewarsa, yanzu haka yana da Pi fiye da guda duba daya da dari biyar, wanda da Labarun Hausa ta yi kiyasi, idan ya sauya Pi dinsa a kudin Najeriya, zai tashi da kimanin N270,000,000,000.

Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button