Duk Namijin Kwarai Yana Son Jin Wadannan Kalmomin Daga Bakin Matarsa:
Mata ga wasu kalmomin da babu wani namijin da baya so yaji matarsa ta furta mata su sai dai namijin da bai san darajar soyayar aure ba.
Yana da kyau a kalla duk wata ma
Yana da kyau a kalla duk wata mace tayi kokarin furtawa mijinta akalla kalma guda daya duk rana.
Hakan yana da matukar tasirin da zai inganta Zamantakewar auren su.
Ga wadannan kalmomin kamar haka:
1: Ban taɓa danasanin auren ka ba.
2: Nayi sa’ar samun miji.
3: Ina alfahari da kai.
4: Na yarda da kai 100 bisa 100 mijina
5: Na gode.
6: Allah Ya ƙara buɗi.
7: YI haƙuri.
8:Na tuba.
9: Ka ƙara hakuri dani
10: Ka sanar dani abubuwa da dama a rayuwata.
11: Da duk maza kamarka suke da mata sun huta.
12: Kalamanka kawai suke sani tsuma.
13: Ka shagwaɓani da soyayya
14: Ina godiya da irin ɗawaniyar da kake yi damu.
15: Soyyya da kaunar da kake nuna mini sune suka ɗaukaka matsayina
16: Ina murna idan naga ko naji ka kyautatawa wasu.
17: Dole ke sa nake nesa da kai.
18: Ina kara sonka a kowani daƙiƙa.
19: Kaine mutuncina.
20: Ko a Aljanna dakai nake burin rayuwa na har abada.
Da fatan zaku yi amfani da su ta hanyar data dace, da kuma lokacin daya dace.
Sannan A Kula Da Tsafta Itama Tana Kara Dankon Soyayya.
Sannan Girki Mai Dadi Shima Yana Kara Dankon Soyayya.
Sannan Alkinta Dukiyar Mai Gida Shima Yana Kara Dankon Soyayya.
Sannan Tattala Kayayyakin Abimci Shima Nakara Dankon Soyayya.
Sannan Yawaita Istigifari Shima Yana Cika Zuciyar Megida Da Kawataki Acikinta.
Salatin Annabi Shima Haske Ne Kuma Zai Kara Haskaki Cikim Zuciyar Mai Gida.
Yin Sallah Akan Lokaci Shima Yana Kara Dankon Kauna Dakuma Soyayya.
Yawaita Karatun Alkur’ani Shima Yana Daga Darajarki A Wajen Mai Gida.
Dirkuwasawa Yayin Amsa Ko Bayarwa Ga Mai Gida. Shima Yana Dada Darajarki.
Saka Turare Mai Kamshi. Shima Yaka Kara Soyayya.