News

Dr. Isa Ali Pantami Yayi Allah Wadai Da Dabi’ar Matasan Yanzu A Kasar Nan Na Neman Aikin Gwamnati Maimakon Kama Sana’a

Dr. Isa Ali Pantami Yayi Allah Wadai Da Dabi’ar Matasan Yanzu A Kasar Nan Na Neman Aikin Gwamnati Maimakon Kama Sana’a

Minista Pantami Ya yi Alla-wadai da dabi’ar matasan Najeriya na neman aikin gwamnati maimakon sana’a da kasuwanci.

An dade ana cece-kuce a kasar kan wadanda suka kammala karatunsu ba su iya kare shaidarsu ba, kuma ba su cancanci aikin da ake daukar su yi ba.

Dr Isa Pantami wanda bai ji dadin wannan abin da ya faru ba, a baya ya bayyana cewa hakan na shafar tattalin arzikin kasar nan da kuma kara yawan marasa aikin yi a kasar.

Don haka bMinistan ya bukaci wadanda suka kammala karatu a kasar nan da su kasance masu sana’o’in dogaro da kai, domin hakan zai taimaka wa tattalin arzikin kasar ya dore a maimakon tsayawa sai an samu ayyukan gwamnati.

Ministan sadarwa, Dr. Isa Ali Pantami, ya ce galibin wadanda suka kammala karatu a cibiyoyin Najeriya ba sa iya yin aikin da aka basu.

Vanguard ta rahoto cewa ya koka kan yadda ‘yan Najeriya da suka kammala karatu ke neman aikin gwamnati maimakon shiga harkar kasuwanci wanda hakan zai ba su kwarin guiwar daukar wasu aiki.

Yace:

“Ba za mu iya yin alfahari da iliminmu da tsarinmu ba har sai mun sami damar samar da ɗalibai da masu digiri waɗanda za su iya yin abin da muke so ga ƙasarmu.”

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen bikin bayar da kyaututtuka wanda ya gudana a Katsina a ranar Talata 15 ga watan Fabrairu.

Pantami ya ce:

“Kamar yadda lamarin yake a yau, yawancin matasan mu bayan sun kammala karatu ba su cikin tunanin kasuwanci, kawai suna sha’awar neman aikin gwamnati ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button