Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dalilanta na banbanta mai kudi da talaka a duk lokacin da aka same su da laifi.
Hukumar ta musanta zargin da ake yi mata na cewa ba ta hukunta masu hali lokacin da aka kama su da aikata laifi irin daya da talaka, suna cewa kawai yadda suke mu’amalantarsu ne ya sha banban.
A baya-bayan nan an ta sukar hukumar ne kan dauke ido akan bushashar da ta gudana a auren dan gidan shugaban kasa Yusuf Buhari.
A wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom babban daraktocin hukumar Aliyu Kibiya ya ce ya sabawa koyarwar addinin Musulunci a rika sukar shugabanni a bainar jama’a.
Quote Message: Duk da cewa muna kiran kowa ya aikata daidai a cikin al’umma, amma kuma muna daukar mataki daidai da irin laifukan da ake yi. Ya sabawa dokokin addinin musulunci a hau mimbari a soki shugabanni. Akwai yadda ake jan hankalin shugaba ba tare da sukarsa a cikin bainar jama’a ba, in ji Kibiya…
A wata hirar kuma ta daban a wasu shirye-shiryen gidan rediyon shugaban hukumar Haroun Ibn-Sina, ya ce sun kakkama ‘yan masu kudi da yawa tare da daukar mataki a kansu, kuma har yanzu suna kamawa.