News

Daliban Najeriya Mun Shiga tasku a hanyarmu ta dawowa gida daga Sudan

Wasu daga cikin ɗaliban Najeriya da aka kwaso daga Sudan sun bayyana wa wakilinmu halin da suka shiga tun bayan ɓarkewar faɗa a babban birnin ƙasar, Khartoum.

A daren Alhamis ne ɗaliban suka sauka a filin jirgi na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, bayan shafe sama da mako guda a kan hanya.

Yawancin ɗaliban dai sun sauka a gajiye kuma da ganin su sun ƙosa su isa gida.

“Mun shiga cikin halin tashin hankali sosai da fargaba da rashin kwanciyar hankali.” In ji ta.

Ta ƙara da cewa “mun kwana a zaune cikin bas(mota), kafata ta kumbura, baya da wuyana suna ciwo, babu ruwa, ga ƙishi ga yunwa.”

Shi kuma Kamilu Nuhu Sanda cewa ya yi “mun ga abin da ba mu taɓa gani ba a rayuwarmu, lokaci ɗaya muka tashi muka fara jin ƙarar bindiga, fitsari ma idan za ka yi sai ka bayar da ɗari biyar.”

Zainab Abdulqadir, wadda ke riƙe da jakkarta ta hannu, ta shaida mana cewa ta shiga hali na tashin hankali a tsawon lokacin da ta kwashe tana son baro ƙasar ta Sudan.

Daliban waɗanda suka sauka da misalin ƙarfe 11:30 na dare a filin jiragen sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja na daga cikin kason farko da suka samu ficewa daga Sudan ta ƙasar Masar.

Rukuni na farko na daliban na Najeriya daga Sudan waɗanda ke guje wa yaki sun isa gida ne da talatainin dare, ranar Laraba.

Tun farko a yammacin Larabar ne hukumomin Najeriyar suka bayyana cewa jirgin na farko ya taso daga filin jirgin sama na birnin Aswan.

Jirage biyu ne dai suka sauka a daren na ranar Laraba, inda jirgin saman sojin ruwa na Najeriya ya ɗauko mutum 94, yayin da jirgin kamfanin AirPeace ya ɗauko mutum 283.

Hakan dai na zuwa ne sama da mako biyu bayan ɓarkewar faɗa a Khartoum, babban birnin Sudan

Sudan ta fada cikin wani yanayi ne bayan fito-na-fito tsakanin bangarori biyu na mayaka a kasar.

Alkaluma daga hukuma sun bayyana cewa rayukan daruruwan mutane sun salwanta ya zuwa yanzu, sai dai babu sahihin bayani kan yawan wadanda suka mutun.

Kasashe da dama sun gaggauta wajen ganin sun kwashe ƴan kasarsu, sai dai Najeriya ta fuskanci tsaiko bayan ƙalubale da dama.

A ranar Laraba ne Birtaniya ta sanar da kammala kwashe ‘yan kasarta, a daidai lokacin da jirgi na farko da zai kwaso ‘yan Najeriya mazauna Sudan din ke shirin baro Masar.

Yanzu haka dai akwai sauran dubban ‘yan Najeriyar mazauna Sudan da suke jiran a kwaso su, wadanda galibi dalibai ne da ke karatu a jami’o’i daban-daban na kasar.

Baya ga ɗaliban da ake sa ran za su baro Sudan ɗin ta Masar, akwai wasu da ke a birnin Port Sudan, waɗanda ake sa ran za su tsallaka Saudiyya ta bahar Maliya kafin jirgi ya kwashe su daga Jiddah zuwa gida Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button