DA ‘DUMI ‘DUMI Sanata Kwankwaso na gaf da komawa Jam’iyar APC Mai Mulki.
Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kusa kammala shirinsa na komawa jam’iyyar APC.
Kwankwaso, wanda tsohon Sanata ne mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, bai ji dadin jam’iyyar PDP ba tun bayan tarzomar da aka yi a babban taron jam’iyyar a watan Afrilu a Kaduna.
Taron wanda ‘yan Kwankwasiyya suka tarwatsa, ya biyo bayan ganin cewa dan takarar su na kujerar mataimakin shugaban Jam’iyyar ba zai yi nasara ba.
Sanata Kwankwaso wanda ke goyon bayan Mohammed Jamo Yusuf kan Bello Hayatu Gwarzo, ya dage cewa a bar shi ya kawo mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin daga bangarensa.
Sanata Bello Hayatu Gwarzo yana samun goyon bayan mafi rinjayen masu ruwa da tsaki a shiyyar Arewa maso Yamma da suka hada da Gwamna Aminu Tambuwal, wanda Kwankwaso daman ya zarge shi da shine ya sayawa Bello Hayatu form din takarar a wata hira da BBC tai da kwankwason
Bayan kammala taron da ba a yi shi ba saboda tarzoma, da kuma ganin yadda Kwankwaso ya sha kaye, ya tabbatar da cewa PDP ba ta shirye ta ba shi goyon baya da ‘yan takararsa ba, shi ya sa aka fara tuntubar ‘Yan APC ciki har da Ashiwaju Bola Ahmed Tinubu jagoran Jam’iyyar.
Rahotonni ya tabbatar da cewa, Sanata Kwankwaso ya gana da Tinubu a kasar Saudiyya inda suka yi wata ganawar sirri kan makomar siyasarsa.
Wasu majiyoyi na kusa da Kwankwaso sun shaidawa majiyarmu ta POLITICSDIGEST cewa ya tattauna da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC Mala Buni, gwamnan jihar Yobe.
Jaridar ta ce, dan takarar gwamnan jihar Kano a kakar zaben 2019 da ta gabata Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo, dukkansu Kwankwaso zai koma APC da su da dubban magoya bayansa.
Kwankwaso zai sauya sheka zuwa APC da zaran ya tuntubi kowa da kowa, hukuncinsa na karshe zai biyo ne bayan an kamala babban zaben APC da za a yi a watan Agusta.
Musa Iliyasu Kwankwaso, Kwamishinan Raya Karkara na Jihar Kano, ya bayyana matakin da Kwankwaso ya dauka na shiga jam’iyyar a matsayin abin maraba da shi amma ya gargade shi da kada ya zo ya hargitsa jam’iyyar APC kuma dole ya yarda Gwamna ne Jagoran jam’iyyar a Jahar, kamar yarda shi Abdullahi Umar Ganduje ya bishi a baya. Inji Musa Iliyasu.
A kwanakin baya ne wani faifan bidiyo na hira da Buba Galadima a gidan rediyon DWHausa da aka gani a yammacin ranar Laraba ya zargi PDP da rashin shirin yakar APC.
Galadima ya yi Allah-wadai da PDP, inda ya bayyana ta a matsayin jam’iyyar adawar da bata san komai ba.
PDP ba jam’iyya ce mai adalci ba,suna da wani shirinsu na daban, idan ba ka cikin dandalin su ka manta da samun dama a jam’iyyar kuma duk wanda ya san abin da take yi ba zai zauna a cikinta ba. Inji Buba
Kowa ya san cewa dai Malam Galadima makusanci ne kuma abokin Kwankwaso.
Saifullahi Hassan mai taimakawa Kwankwaso ne ya raba bidiyon a WhatsApp da Facebook.
Mutane da yawa sun ga faifan sautin sa na DW inda ake zargin da sanin kwankwason ya wallafa abun a matsayin sa na mai magana da yawun Kwankwaso.