DA DUMI-DUMI: Kotu ta tabbatar da Danzago a matsayin shugaban APC na Kano, ta umarci bangaren Ganduje da ya biya tarar N1m
Wata babbar kotun babban birnin tarayya Abuja karkashin jagorancin mai shari’a Hamza Muazu ta tabbatar da cewa bangaren jam’iyyar APC a Kano karkashin Sanata Ibrahim Shekarau sun gudanar da tarukan unguwanni da kananan hukumomi a jihar.
A ranar 30 ga Nuwamba, alkalin kotun ya amince da duk wata bukata da bangaren Malam Shekarau ya nema, inda ya nemi a bayyana cewa Bangaren Ganduje basu gudanar da zaben shugabancin Jam’iyya ba.
Da yake yanke hukuncin a ranar Juma’a, alkalin kotun ya yi watsi da bukatar da suka gabatar tare da cin tarar su Ganduje Naira miliyan 1 bisa samunsu da laifin gabatar da kudiri na rashin gaskiya da kuma batawa Kotu lokaci.
Kotun ta ci gaba da cewa taron kananan hukumomi da bangaren Shekarau suka gudanar yana nan daram kuma suna da hurumin zaben exco na jiha.
Wadanda suka shigar da karar sun hada da Muntaka Bala Sulyman mai mutane 17,980 na jam’iyyar, yayin da wadanda ake karan su ne APC a matsayin wanda ake kara na daya, Mai- Mala Buni, Shugaban riko; Sen. John Akpanudoedehe, sakataren kasa da; Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, a matsayin wanda ake tuhuma na hudu.