Bayan rantsuwa da Alkur’ani, Sheikh Abdujabbar ya fara kare kansa a kotu.
Nasiruddeen Abdullahi Tungush
Bayan hutun mintuna 30 da Mai Shari’a Alƙali Ibrahim Sarki Yola ya bayar a zaman shari’ar na yau, Malam Abdujabbar Kabara wanda aka gabatar dashi gaban kotun bisa tuhumar kalaman ɓatanci da tunzuri ya cigaba da bayanan sa na kariya a gaban kotu.
Malamin ya ci gaba da bayanai daga littafai cewa ba ya yiwuwa a kira batanci da ridda kai tsaye, kaman yadda kuma baya halatta a zubda jinin musulmi sai akan abubuwa guda 3. Ya bayyana su kamar haka; Katangaggen da yayi zina, wanda ya kashe rai a kashe shi, da kuma wanda ya bar Musulunci kuma yake yakar musuluncin.
Game da batun dake cikin tuhuma ta farko, wato lafazin fyade da ya ambata, Malam Abduljabbar yace bashi ne ya fada ba, shi korewa yayi, kuma ba shi ne ya fara fadar cewa zahirin hadisin, abinda yake nasabtawa Annabi SAWA kenan.
”Malaman da suka fito da ma’anar hadisin da irin fahimtar da nayi suka kore hadisin sun hada da imamu Malik da Abu Hanifa da sauransu.” inji Malam Abdujabbar
Ya kara da cewa ”a cikin mu’ujamul Kabir J 11 shafi na 303 (Bayan ya koro isnadi), Annabi yayi sulhu da mutanen Khaibar cewa ……………..(Har zuwa fadin sa) yace a kawo masa dukkan iyalansu, aka zo masa da Safiyya tana amarya, Yana ganin ta sai yace akai masa ita tantin sa, (A ruwayar suka ce sai) aka bi da ita takan gawawwakin yan uwansa, Bilal yace yayi hakan ne saboda ya kona zukatansu, sai Annabi ya shiga tentin da take ya kwanta da ita”
Bayan Malamin yayi bayani masu tsayi kan hadisin, Lawyan dake kare wanda ake ƙara Barr. A.O Mohammed SAN ya bijirar da tambaya ga malamin kan abubuwan da aka rubuta a jikin takardar tuhuma da hadisin ko shin ya yarda da wadannan maganganun?
Malamin yace bai yadda da su ba shi yasa ma yake kore su, inda anan ne lawyan ya sake tambayar sa cewa;
”Cewa kace, kaman yadda yazo a kunshin tuhuma ta 2, Nana Safiyya ta fito ne a rabon wani, amma ma’aiki SAWA yaji labari sai ya karbe ta ya musanya masa da kuyanga 7, shin kai ne ka fadi wannan ko kuma a wani wuri ka karanta?” Inji Lawyan wanda ake ƙara.
”Wannan magana da na fada Ni korewa nake ba tabbatar wa ba, a cikin Muslim tazo, domin kuwa yace, (A kawo masa ita bayan ya bada ita, ya karbe ta ya musanya masa), cewar ya bayar yasa an karbo, babu shakka kwace ne, kuma haka yake a ruwayar Zuhair bn Abi shaibah” inji Wanda ake ƙara Malam Abduljabbar.
Malamin ya sake bayyana cewa shi ma’anar hadisi ya fada ba wai lafazi ba, shiyasa ya fara shimfida da bayanin halaccin yin fassarar hadisi da ma’ana a farkon fara kariyar sa.
A daidai wannan gaɓa ne Lawyan wanda ake ƙara ya nemi kotu da ta daga zaman zuwa rana ta gaba dan cigaba da kariyar, kuma lawyoyi masu gabatar da kara basuyi suka ba. Mai Shari’a ya dage zaman zuwa 17/3/2022 dan cigaba da sauraren kariya daga bakin malamin.
Ga Bidiyon Ku Kalla Rubutu Da Bidiyo Daga Jarida Radio
3/3/22
https://youtu.be/yLgurouo_YU