Matar Abba Kyari ta yanke jiki ta faɗi a kotu
Ramatu Yakubu Kyari, matar dakataccen Mataimakin Kwamishinan Ƴan Sanda, DCP Abba Kyari, a yau Litinin ta yanke jiki ta faɗi a cikin harabar Babbar Kotun Taraiya da ke Abuja, jim kaɗan bayan kotun ta ɗage yanke ƙwarya-ƙwaryan hukunci a kan belin sa.
Mai Shari’a Emeka Nwite ne ya ɗage zaman zuwa 28 ga Maris ya kuma umarci a maida Kyari da sauran waɗanda a ke zargi a ci gaba da tsare su a wajen tsare masu laifi na Hukumar NDLEA.
Matar, sanye da bakin Hijabi ta yanke jiki ta fadi ne lokacin da jami’an Hukumar NDLEA ɗauke da bindigogi su ka rasa ƙeyar Abba Kyari da sauran waɗanda a ke zargi zuwa wajen kotun.
Wasu jami’an NDLEA da lauyoyi su ka yi gaggawar dauke ta daga wajen, kuma su ka shigar da ita daya daga cikin ofishohin dake cikin kotu.
Sai dai an yi kokarin samar mata abin shaka, lokacin da matan da suka rako ta kotu suka ce ta na fama da cutar nimfashi ta asma.
Hakan ne ya sanya jami’an NDLEA ɗin su ka samu tsaikon tasa ƙeyar waɗanda a ke zargi, in da su ka jira Kyari ɗin ya je 2ajaen mai ɗakin nasa har tsawon kimanin mintuna 45 san nan ya zo a ka tafi da su.
https://youtu.be/L1UdUoW_zCk