Bidiyon Yadda Giwaye Suka Addabi Manoman Yankin Gamboru Ngala A Jihar Borno
Manoma a yankin Gamboru Ngala na jihar Borno da ke da iyaka da kasar Kamaru a Najeriya, sun yi kira ga hukumomi da su kai musu dauki saboda barna da giwaye suke yi wa gonakinsu a yankin.
Bayanai sun yi nuni da cewa giwayen sukan far gonakin mazauna yankin ne da tsakar dare su cinye musu amfanin gonakinsu.
“Gaskiya ba zan iya ce maka ga yawan giwayen nan ba. Yanzu gaba daya garin da daddare za mu fita mu kona tayu, muna kade-kade don mu kore su.” Alhaji Katomi, daya daga cikin mazauna yankin ya ce.
Ire-iren kayan amfanin gona da suke lalatawa sun hada da dawa, wake da sauran shuke-shuke a cewar mazauna yankin.
“Rokonmu shi ne gwamnati ko hukumomi masu zaman kansu, su tallafa mana.” In ji Alhaji Abba Greman Ngala.
Hon. Abdulrahman Abdulkarim, mai taimakawa Gwamna na musamman, wanda ya fito daga yankin na Gamboru Ngala, ya ce sun samu labarin wannan lamari kuma suna kokarin duba yadda za su magance wannan matsala, domin wannan ba shi ne karon farko da hakan ke faruwa ba.
Saurarin cikakken rahoton Haruna Dauda Biu daga Maiduguri:
https://youtu.be/ool3Lua58rA