Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta ce ta ceto tare da kashe gobarar da ta barke a wata babbar mota makare da buhunan siminti a yankin Nsukka na jihar Enugu.
Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB ne, suka banka wa motar wuta a yayin da suke aiwatar da dokar zaman gida a jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Daniel Ndukwe, ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin a Enugu cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar ranar Litinin, 6 ga watan Yuni, a kan titin 9th-Mile-Nsukka-Obollo Afor.
Mista Ndukwe ya ce ba a rasa rai a lamarin ba inda ya kara da cewa.
“Da sanyin safiyar ranar 6 ga watan Yuni, jami’an ‘yan sanda yayin da suke sintiri na karfafa gwiwa a cikin Nsukka, sun lura da wata babbar motar dakon kaya dauke da buhunan siminti da ke cin wuta a mahadar bakin teku da ke titin Obollo Afor mai lamba 9-Mile-Nsukka-Obollo Afor. .
“Gobarar wacce ta kone kan babbar motar, daga karshe jami’an ‘yan sanda ne suka kashe su tare da taimakon wasu masu kishin al’umma a yankin.
“Ba a rasa rai ba, yayin da aka tsare motar da buhunan siminti,” in ji shi.
Kakakin ‘yan sandan ya ce an fara bincike don gano ainihin musabbabin tashin gobarar.