News

BIDIYO: ’Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A wannan Sabon Bidiyo Da Suka Fitar.

’Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Buhari

’Yan Bindiga Sun Yi Barazanar Sace Shugaban Kasa Muhammadu Buhari A wannan Sabon Bidiyo Da Suka Fitar.

A sabon bidiyo da Aminiya ta gani, ’yan ta’addan da suka yi garkuwa da fasinjoji sama da 60 a wani jirgin kasa da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna tun a ranar 28 ga watan Maris, sun yi barazanar sacewa da kashe Shugaba Buhari da kuma Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Wannan barazana dai na zuwa ne makonni bayan da wasu ’yan ta’adda suka kai hari kan tawagar motocin shugaban Najeriyar, a yayin da suke kan hanyar zuwa garin Daura a Jihar Katsina, gabanin tafiyarsa hutun Sallar layya.

Sai dai sanarwar da Fadar Gwamnatin Najeriya ta fitar, ta tabbatar da cewa Buharin ba ya cikin ayarin motocin a wancan lokaci, inda ta ce kashin farko ne na jami’an da za su hidimta wa shugaban kasar yayin hutunsa na Babbar Sallah a Daura.

A cikin bidiyon, ’yan ta’addan sun kuma yi bugun kirjin cewa za su ruguza kasar nan, sannan za su kashe wasu daga cikin fasinjojin da ke hannunsu su kuma sayar da sauran.

Daya daga cikin ‘yan ta’addan ya yi barazanar cewa, idan har gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to za su mayar da yankin tamkar mahauta.

“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Najeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane a nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnoninku za su zo gabanmu.

“Wadannan da kuke gani a nan za mu rike wasu a matsayin bayi mu sayar da su kamar yadda jagoranmu ya fada muku a baya,” inji shi.

Ya ci gaba da cewa a cikin harshen Hausa: “Kamar yadda aka sayar da ’yan matan Chibok, za mu sayar da wadannan a matsayin bayi.

“Idan ba ku biya mana bukatunmu ba, za mu kashe wadanda muke da bukata mu sayar da sauran. Da yardar Allah, El-Rufai da Buhari za su shigo hannunmu.”

Aminiya ta ruwaito yadda ’yan ta’addan suka saki wasu daga cikin fasinjojin jirgin kasa na Kaduna bayan karbar fansa ta kimanin Naira miliyan 100 kan kowane mutum guda.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button