Religion

BIDIYO: Yadda Wani ɗalibi ya haɗa maganin ciwon ciki da ayoyin Allah Ta’ala dake Alƙur’ani mai girma.

BIDIYO: Wani ɗalibi ya haɗa maganin ciwon ciki da ayoyin Allah Ta’ala dake Alƙur’ani mai girma.

A wannan Course ɗin mai suna “The Qur’an and Human Sciences” an koya mana yadda za ka haɗa magunguna da ayoyin Allah Ta’ala dake ƙur’ani, kuma maganin da idan ka haɗa, ka sha za ka warke da yardar Allah Ta’ala.

Bari na fara baku misali da maganin ciwon ciki na ruwa. Ga yadda ake haɗa maganin.

Da farko za ka siyo zuma wacce ba a yi mata mis da komai ba, sai ka samo tsarkaken ruwa, amma an keɓance ruwan sama a nan gun. An fi so idan za a haɗa maganin a samo ruwan sama, ba wani ruwa daban ba. Idan babu ruwan sama sai ayi amfani da wani ruwan daban, Saboda lalurar rashin ruwan sama.

Sai a cakuɗa ruwan saman da zumar da aka siyo. Kada a manta zumar da ba ayi mata mis ba. Bayan an cakuɗa su waje ɗaya, ma’ana an haɗa zumar da ruwan waje guda, sai a sha.

Amma da sharaɗin za a sha sosai. A sha a ƙoshi. Kada a sha kaɗan, za a sha sosai ne.

Dalilan da suka kawo na wannan maganin da ayoyi su ne kamar haka. Dalili a kan zuma;

يَخْرُجُ مِن بُطُونِهَا شَرَابٌ مُّخْتَلِفٌ أَلْوَانُهُ فِيهِ شِفَاءٌ لِّلنَّاسِ

Yana fita daga cikin ta abin sha mai launuka mabanbanta, to a cikinsa akwai waraka ga Mutane. Ana magana ne a kan zuma.

Dalili a kan ruwan sama;

وَنَزَّلْنَا مِنَ السَّمَاءِ مَاءً مُّبَارَكًا

Kuma muka saukar daga sama ruwa mai albarka.

Dalilan a sha a ƙoshi;

كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا

Ku ci, ku sha, kuyi hani’an.

To duk wanda ya yi kamar yadda aka faɗa mishi, to In sha Allahu zai samu waraka.

Daga ƙarshe za mu rufe da wannan ruwayar da tazo daga Sayyidina Ali (RTA); Wani mutum yazo wajen Sayyidina Ali (RTA) ya ce masa, cikinsa na mishi ciwo, sai Sayyidina Ali ya ce mishi kana da mata. Sai ya ce mishi “eh” ina da mata, sai Sayyidina Ali ya ce mishi ka nemi wani abu tsarkakakke daga dukiyarta, ma’ana kuɗi na halas, ka siyo zuma da ita ka zuba a ruwan sama, sannan ka sha, zaka warke, saboda na ji Allah mai girma da ɗaukaka yana cewa a cikin Littafinsa, mun Saukar daga sama ruwa mai Albarka, ya ƙara da cewa, yana fita daga cikin ta abin sha mai launuka mabanbanta, to a cikin sa akwai waraka ga mutane.

In Sha Allah tun da mun taɓo ɓangaren “Medicine”, nan gaba kuma za mu taɓo wani ɓangare daban. Sha’anin ƙur’ani mai girma ya zarce duk inda tunanin ka zai harba Malam.

Sunan wannan ɗalibi Mustapha Muhammad Rajab, ya yi wannan rubutun ne a Timeline ɗin shi na Facebook kwanaki huɗu (4) da suka gabata.

Ɗalibi Mustapha Muhammad Rajab.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button