Sojoji sun kuɓutar da ɗaya da ga cikin ƴan matan Chibok tare da ɗanta
Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta ceto wata yarinya Mary Ngoshe, wadda ake kyautata zaton tana ɗaya daga cikin ƴan matan da aka sace daga makarantar Sakandaren ƴan mata ta gwamnati ta Chibok, a Borno.
Rundunar ta bayyana hakan ne a yau Laraba ta sahihin shafin ta na Twitter na rundunar sojojin Najeriya, ‘@HQNigerianArmy,’.
Rundunar ta ce dakarun rundunar sojoji ta bataliya ta 26 da ke sintiri a kewayen Ngoshe, a Borno sun kama wata mai suna Ngoshe da ɗanta.
“A na kyautata zaton tana daya daga cikin ‘yan matan da aka sace daga GGSS Chibok, a cikin 2014. Ana ci gaba da bincike a kan lamarin,” in ji bayanin.
Rundunar ta kara da cewa: “A ci gaba da farmakin da dakarun Operation Desert Sanity, tare da hadin gwiwar CJTF suka yi, sun sake yin wata gagarumar nasara a ranar Talata.
“Wannan ya kasance yayin da aka kashe ‘yan ta’addar ISWAP a kusa da Gurzum, a Borno.
“An lalata kasuwar ‘yan ta’adda da sansanoni. An kwato makamai, da sauransu,” in ji bayanin.
Gadai Karin Bayani Game Da Batun